Sunday, February 14, 2021

Kadan Daga Cikin Aika-Aikar Abduljabbar Kabara

 Kadan Daga Cikin Aika-Aikar Abduljabbar Kabara 





KADAN NE CIKIN DARURUWAN ISKANCIN DAN KABARA, ALLAAH KA ISARWA SAHABBAN ANNABINKA SAW AKANSA. 

Kadan Daga Cikin Aika-Aikar Abduljabbar Kabara!


Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai


Assalamu Alaikum


Jama'ah ga kadan daga laifukan Abduljabbar, yana da kyau mu san su:


1. Yace Nana Aisha (RA) ba tayi imani da mijinta Annabi ba kwata-kwata.


2. Yace sayyadina Usman (RA) Dan jari hujja ne, a lokacinsa masu kudi suka kara kudi talakawa kuwa suka kara talaucewa, a bisa haka ne Sahabbai suka taru suka kashe shi.


3. Yace Abdullahi Dan Umar (RA) munafiki ne mai karbar cin hanci da rashawa.


4. Yace Sahabin Manzon Allah Abu Hurairah (RA) tataccen makaryaci ne da ya kitsa Hadisan karya, ya dangana su ga Annabi (SAW), kuma a yau suka cika littafai.


5. Yace Sahabin Manzon Allah (SAW) Anas (RA) makaryaci ne kuma munafuki.


6. Yace Sahabiyah Ummu Sulaim (RA) Mahaifiyar Anas (RA) mahaukaciya ce tana da tabin hankali, kuma ita ce Fulana da aka ambata a wani Hadisi.


7. Yace Annabi (SAW) ya dauki dan zina a matsayin sakatarensa, yana rubuta masa wahayi, kuma bai yi imani da Annabin ba har ya mutu.


8. Yace munafukai ne suka kewaye Annabi (SAW), kuma sune suka hana ya rubuta yadda yake so su rayu bayansa, kuma su kayi munafurcin rusa wasiccinsa na ranar Ghadir.


9. Yace Nana Aisha da Hafsah (RA) suna ta kulle-kulle lokacin da Annabi (SAW) yana rashin lafiya kafin watafinsa.


10. Yace Alkur'anin da yake hannun mu ba ingantacce ba ne.


11. Yace karya ne Annabi bai je sama Mi'iraji ba. Kuma Alkur'ani ma ya tabbatar da Mi'iraji.


12. Yace karya ne babu tambayar kabari, da azabar kabari da tashi daga cikinsa.


13. Yace babu mutanen da ke karyata junansu kamar Sahabban Annabi (SAW).


14. Ya kundumawa Annabi Muhammad (SAW) zagi, yace a WhatsApp aka turo masa yana da audio, amma har yau bai fitar da audion ba😭😭😭!


Wannan dai bai kai kashi biyar cikin dari na aika-aikarsa ba. Don haka Ya Allah, ka shaida, kuma duniya ta shaida cewa, na tsani Abduljabbar Kabara, tare da duk mai goya masa baya, kamar yadda ya tsani Annabi (SAW) da Iyalansa da Sahabbansa da bayin Allah nagari. 


Ya Allah ka jaddada la'ana a gare shi, amin.



No comments:

Post a Comment

Pages