Wednesday, February 17, 2021

Jihar Kano ta ware kudade N83.5m don yiwa dabbobi rigakafin

 



- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa, ta bada kwangilar yiwa dabbobi rigakafi 


- Gwamnatin ta ware makudan kudade domin ta karfafa harkar kiwo a jihar ta Kano 

- Manufar rigakafin zai zama inganta kiwo da karfafa sana'ar kiwo ga makiyayan Kano A ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da kwangilar Naira miliyan 83.4 don rigakafin dabbobi, The Nation ta ruwaito. Yarjejeniyar ta hada da samar da kwalabe 8,250 na maganin rigakafin Bovine Pleuropneumonia (CBPP) da kuma kwalabe 20,000 na maganin rigakafin Peste des Petits Ruminants (PPR). 

Shirin allurar rigakafin a duk fadin jihar, wanda zai fara nan da wasu makonni zai dauki shanu 800,000 da kuma kananan dabbobi miliyan 1 a kowace shekara. 


Shirin allurar rigakafin za a aiwatar da shi ne ta hanyar shirin Bunkasa Aikin Noma da Makiyaya (KSADP), Kwararren Masanin Sadarwa Ameen K. Yassar, wanda ya bayyana a wata sanarwa a ranar Talata. Ya bayyana cewa allurar rigakafin zata taka muhimmiyar rawa wajen inganta karfin dabbobi don yaki da cututtuka da kuma kula da jin daɗi da samar da manya da ƙananan dabbobi. Ya bayyana cewa ba a gudanar da rigakafin dabbobi a jihar Kano ba a cikin shekaru uku da suka gabata kuma a sakamakon haka, yawancin al'ummomin makiyaya a jihar na fama da asarar dabbobi sosai. Kodinetan ayyukan na jihar, Malam Ibrahim Garba Muhammed, wanda ya sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin hukumarsa, ya bayyana cewa an yi hakan ne don hana dubban iyalai makiyaya a daya daga cikin jihohin da suka fi yawan jama’a a Najeriya rasa ayyukansu. 



No comments:

Post a Comment

Pages