Gwagwarmaya: Hajia Gambo Sawaba ƴar siyasa Mace da ta fi shan ɗauri a Najeriya
Sunan Hajia Gambo Sawaba ba baƙon suna bane a tarayyar Najeriya, la’akari da irin gwagwarmayar da ta yi akan harkokin siyasa da kuma ganin an baiwa mata haƙƙinsu a cikin al’amuran rayuwa da siyasa. Hakan ne ya sanya ta zama Mace ƴar siyasa a faɗin Najeriya da ta fi shan ɗauri a gurin mahukunta.
Haka kuma abu ne mai wuya a tsallake sunan Gambo Sawaba idan aka zo kan batun siyasar Najeriya. Domin ita ce mace ɗaya tilo ƴar siyasa da ta yi ƙaurin suna a arewacin ƙasar nan har zuwa shekarun 1990.
Wacece Hajia Gambo Sawaba?
An haifi Gambo Sawaba a ranar 15 ga watan Fabrairun shekarar 1933 a birnin Zaria da ke jihar Kaduna, ta kasance mai rajin kare haƙƙin mata, ƴar siyasa sannan kuma mai taimakon al’umma.
Hajia Gambo Sawaba ta tsunduma fagen siyasa ne tana da shekaru 17 kacal a duniya. Kuma ta kasance ƴar jam’iyyar adawa a wancan lokacin ta Northern Elements Progressive Union (NEPU) tare da Malam Aminu Kano duk da cewa jam’iyyar Northern People’s Congress (NPC) ce ke da matukar goyon baya a arewacin Najeriya.
Ta riƙe muƙamin shugabar mata a jam’iyyar inda ta tsaya tsayin daka don ƙwatar wa mata ƴancinsu na yin zaɓe da tsayawa takara.
Ana iya cewa ta taka rawar da babu macen da ta taba irinta a arewacin Najeriya a wancan lokacin musamman a lokacin da ta hau kan mumbari a wani taron siyasa da maza suka mamaye a shekarar 1950 kuma ta yi jawabi mai jan hankali dangane da siyasar Najeriya.
Wannan ya ƙara fito da ita kuma ya zamar mata wani ginshiki na rayuwarta ta siyasa.
Gambo Sawaba ba ta taɓa riƙe wani muƙami na gwamnati ba amma ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ƴan ƙasa da ƙwatarwa talakawa da mata haƙƙinsu sannan ta ƙalubalanci nuna wariya da ake yi wa mata a arewacin Najeriya.
Ta yi amfani da muryarta wajen sukar auren dole da auren wuri da ake yi wa mata a arewacin Najeriya.
Wannan ƙarfin hali da rashin tsoro na Gambo ya janyo mata ce-ce-ku-ce inda har jami’an tsaro suka taɓa kamata.
Gogewarta a siyasa ta ƙaru bayan da ta haɗa kai da fitacciyar ƴar siyasar nan kuma mai fafutukar kare haƙƙin mata Oluwafunmilayo Ransome-Kuti ta kudancin Najeriya.
Hajiya Gambo Sawaba ta rasu a shekarar 2001 bayan doguwar jinya.

No comments:
Post a Comment