Bidiyon rikicin da aka yi tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan
Rikici ya barke tsakanin yan kabilar yarabawa da hausawa mazauna garin Ibadan a jihar Oyo - Faifan bidiyon lamarin ya nuna matasa suna hayaniya wasu cikinsu dauke da sanduna da katakai - Kazalika, jami'an yan sanda sun hallara wurin suna kokarin kwantar da tarzoma Rikici ya barke tsakanin Hausawa mazauna garin Ibadan da ke jihar Oyo da Yarbawa masu garin kamar yadda bidiyon da The Punch ta wallafa ya ke nunawa. An hasko cincirindon matasa sun taru a wai wuri dauke da sanduna da katakai a hannayen wasu daga cikinsu suna ta hayaniya da ke nuna ransu ya baci.
Akwai kuma jami'an tsaro na yan rundunar yan sandan Nigeria a kalla guda takwas a cikin taron matasan suna kokarin kwantar ta tarzomar da ta tashi.
Tension As Yorubas And Hausas Clash In Ibadan pic.twitter.com/bRVh54XCbU
— Punch Newspapers (@MobilePunch) February 12, 2021

No comments:
Post a Comment