Na Amfana Da Dangote Duk Da Yaci Amanar Soyayyar Mu -Inji Budurwar Dangote Yar Amurka
Wata tsaleliyar mata ‘yar kasar Amurka mai suna Bea Lewis ta tona wani soyayya da ta yi da Hamshakin Attajiri, Aliko Dangote a Kasar Amurka, wanda ta ce ya ce amanar ta da soyayyar da ke tsakanin su sau dubu-dubu.
Kamar yadda PREMIUM TIMES ta bayyana cewa Bea Lewis ta saka hotunan ta da Dangote rungume da juna, sannan ta rubuta cewa Dangote ya rika wulakantata akai akai fiye da sau dudu-dubu, sai dai kuma ta amfana da shi matuka domin a zamanta da shi ta fahimci harkar kasuwanci, tattali da tsananta yin hakuri.
” Hira kawai da na rika yi da attajiri irin Dangote, fitacce a duniya yakan kwantar min da hankali. Sannan kuma na koyi abubuwa da dama a rayuwa, kuma na samu daukaka da arziki masu yawa.
Lewis ta kara da cewa a dalilin Dangote, ta daina aikin saida tuwo-tuwo, ta fada harkar siyan hannayen jari, sannan kuma ta mallaki gidaje biyu nata, kuma ta dilmiya cikin harkar kasuwanci gadangadan.
” Wani abu da na koya a zama na da Dangote shine yadda ya rika tausa ni yana min khuduba da in rika hakuri a cikin al’amurorina, in rika kama kai na da kuma yin tawali’u a koda yaushe.

No comments:
Post a Comment