Friday, January 8, 2021

Mai laifi ya bayar da bayani mai ban al’ajabi kan yadda ya kashe budurwarsa

 


- Yan sanda sun kama wani mutumi da ya kashe budurwarsa don kudin fansa a jihar Osun 


- A cewar hukumar tsaro, wanda ake zargin yak ware wajen siyar da sassan jikin dan adam 


- Kwamishinan yan sandan jihar ya ce ana kokari don ganin an kama sauran mutanen Wani mutum mai shekaru 31 a jihar Ogun, Tajudeen Monsuru ya tona cewa shi ya kashe budurwarsa, Mutiyat Alani don kudin asiri.


 A wata hira da jaridar Daily Trust, Tajudeen ya ce ya shake budurwar har lahira a ranar da ta zo gidansa sannan ya yanke kanta don yin asirin kudi. 


Ya ce yan uwan budurwar basu san cewa ta kai ziyara gidansa ba sannan cewa babu wanda ya zarge shi a lokacin da ake neman ta. 


Iyayen budurwar sun kai karar lamarin zuwa hedkwatar yan sanda a Iwo cikin shekarar da ta gabata sannan aka kaddamar da batan marigayiyar. 


An tura lamarin zuwa ga sashin bincike na sirri a hedkwatar yan sanda da ke Osogbo, babbar birnin jihar don yin bincike. Kwamishinan yan sanda a jihar, CP Wale Olokode ya ce an kama wanda ake zargin ne ta binciken sirri. 

Olokode ya ce wanda ake zargin ya kuma kashe wani Akinloye Ibrahim da wasu da dama don kudin fansa. Ya ce wanda ake zargin ya kuma kware wajen siyar wa da matsafa sassan jikin dan adam. 

No comments:

Post a Comment

Pages