Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya sake lalacewa a dokar daji bayan ya kinkimo fasinjoji
Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya sake samun matsala a Ranar Lahadi
-An dauki kimanin sa’o’i uku ana gyara kafin wannan jirgin kasa ya tashi
-A baya jiragen nan sun taba mutuwa a dokar daji bayan an dauko fasinja A ranar Lahadi, 3 ga watan Junairu, 2020, jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya sake lalacewa, Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto. Rahoton ya bayyana cewa jirgin kasan ya lalace a hanya ne bayan dawowa daga garin Kaduna.
Bayan an dauko fasinjoji daga Rigasa, jihar Kaduna, an shirya za a tafi Idu, garin Abuja, sai wannan jirgi ya mutu a daidai kauyen da ake kira Akere. Jaridar ta ce a wannan kauye ne kanikawan hukumar jirgin kasan Najeriya na NRC su ka shafe tsawon sa’o’i uku su na ta kokarin gyara jirgin.
Da aka tuntubi wani jami’in da ke kula da jigilar jirgin kasan tsakanin Abuja zuwa Kadunan, Victor Adamu, ya ce wata karamar matsala su ka samu. Ya ce: “’Yar karamar matsala ce kuma an gyara ta. Abin ya faru ne a Akere, yayin da jirgin ke hanyar zuwa Idu, Abuja daga Rigasa a jihar Kaduna.” Ba wannan ne karon farko da jirgin ya lalace a tsakiyar hanya ana tafiya ba. Idan za a tuna, akwai lokacin da sai da gwamnati ta fito ta ba jama’a hakuri. Kwanakin baya, Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya nemi afuwar jama’a, sannan ya umarci kamfanin CCECC ya gyara wadannan jirage.

No comments:
Post a Comment