Saturday, January 2, 2021

Dan sandan Najeriya da bai taba taba karbar Cin Hanci ba ya ajiye aiki saboda rashin karin girma

 



Dansandan Najeriya, Francis Osagie Erhabor da bai taba karbar cin hanci ba ya sanar da ajiye aikinsa saboda rashin masa karin girma.

 

Ya bayyana cewa shekarar sa 30 tana aiki amma sau 5 aka taba masa karin girma inda a yanzu yana matsayin DPO. Yace yana da shekaru 17 ya fara aikin.


Saidai yace yayi nadamar bata lokacinsa a aikin dansandan wanda ya shiga da niyyar aiki tukuru dan kawo canji a kasarsa amma aka rika nuna son kai da siyasa da kuma rashin cancanta wajan karin mukami.


Ya bayyanawa Igbere TV Cewa, an bashi cin hancin Miliyan 864 amma ya ki karba kuma baya nadamar yin hakan duk da cewa abokan aikinsa sun rika kiransa sa sakarai.


No comments:

Post a Comment

Pages