- Cutar Korona ta sake waiwaye na biyu, bayan kimanin shekara 1 da bullarta a Najeriya
- A ranar Juma'a, mutane 12 suka rasa rayukansu sakamakon muguwar cutar
- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake Lockdown Kwamishanar lafiyan jihar Kaduna, Hajiya Amina Mohammed Baloni, ta shiga jerin ma'aikatan gwamna El-Rufa'i da suka kamu da muguwar cutar Coronavirus.
Amina Baloni ta bayyana kamuwar da cutar ranar Alhamis, 8 ga Junairu a shafinta na Twitter.
Ta bayyana cewa tuni ta killace kanta domin jinya. Hakazalika ta yi kira ga jama'a su dau wannan cuta da gaske ta hanyar amfani da takunkumin rufe baki, wanke hannu da kuma gujewa taron jama'a. Tace: "Sakamakon sanarwan da na samu cewa na kamu da COVID-19, na shiga killace kaina da kuma jinya." "Ina kyautata zaton samun waraka da wuri daga wannan cuta." "Ina kira ga kowa mu dau matakin kare kai da COVID19 irinsu rufe baki, yawan wanke hannu da sabulu da ruwa ko kuma sinadarin tsaftace hannu, da kuma gujewa dandazo."

No comments:
Post a Comment