Thursday, January 7, 2021

Babu Adalci A Sukar Da Mutane Ke Yawan Yi Min Amma Ko Kadan Bana Damuwa -Rahama Sadau

 Babu Adalci A Sukar Da Mutane Ke Yawan Yi Min Amma Ko Kadan Bana Damuwa -Rahama Sadau 




Fitacciyar jaruman fina finan nan wato Rahama Sadau ta amsa wasu tambayoyi da suka shafi rayuwarta a wani shiri da tayi a manhajar tuwita inda ta bada damar a yi mata tambayoyi. 




Da aka tuntube ta ko zata bar harkar fim saboda aure, Jarumar ta kada baki da cewa bata fahimci dalili da yasa ake tsangawar mata da ke harkar fina-finai ba idan aka kwatanta da takwarorinsu da ke wasu sana’o’in. 






Don me mutum zai dena fim saboda aure? Shin yin fim ba aiki bane? Me yasa ba a ganin laifin mata da ke wasu ayyukan sai dai yan fim? Misali kamar aikin jarida.” #AskRahama

Jarumar dai bata nuna wata alamar cewa zata bar harkar fim ba domin aure.



No comments:

Post a Comment

Pages