Sarauniyar Bakaken Fata
Daga Mutawakkil Gambo Doko
Misis Gatwech Nyakim wadda yanzu haka ta shahara a shafin yanar gizo na "Istagram" inda take da Mabiya (Followers) kusan Miliyan daya an yi Ittifakin ita ta fi kowacce bakar fata baki a duniya, wanda asalin Iyayenta 'yan kasar Sudan ta kudu ne (South Sudan).
An haifi Misis Gatwech Nyakim a ranar 27 ga watan Janairu, 1993 a garin Gambela na kasar Ethiopia.
Bayan da yakin Basasa ya barke a kasar Sudan sai iyayenta suka yi gudun hijira zuwa kasar Kenya inda daga bisani suka koma garin Gambela na kasar Ethiopia inda nan ne aka bawa iyayenta mafakar siyasa har suka haifi Ms Nyakim.
Daga bisani dai iyayen na Nyakim sun sake yin gudun hijira zuwa kasar Amurka a lokacin Nyakim tana da shekara 14, Iyayenta sun zauna a Buffalo na birnin New York kafin daga bisani su motsa zuwa garin Minnesota na kasar ta Amurka.
Nyakim ta shiga Jami'ar "St Cloud state University) inda a nan ne ta fara shahara a lokacin da ta fito a fastar wani fim na Jigsaw 2017, inda ta ja hankalin mutane da dama.
Haka kuma tana alfahari da bakar fatar da Allah ya yi mata, kuma ta kasance mai Kalubalantar mutanen da suke maida fatar su zuwa fara.


No comments:
Post a Comment