Tuesday, June 2, 2020

An Fara Almajiranci Tun Zamanin Annabi SAW, Don Haka Ba Na Goyon Bayan Hana Bara Da Gwamnonin Arewa Suke Yi, Cewar Rochas Okorocha




An Fara Almajiranci Tun Zamanin Annabi SAW, Don Haka Ba Na Goyon Bayan Hana Bara Da Gwamnonin Arewa Suke Yi, Cewar Rochas Okorocha

Daga Salisu Magaji Fandalla'fih
Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya soki Gwamnonin Arewa da suke hana Almajirci a jihohinsu.
Okorocha ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da kafar watsa labarai ta BBC Hausa, inda ya ce idan ka duba an fara Almajirci ne tun zamanin Annabi S.A.W.

Ya ce inganta harkar shi ya dace kuma bai dace in an gan su a maida su jihohin su ba.

Ya ce domin idan sun je jihohin nasu ma za su yi, dan haka yana kira ga Gwamnoni a hada hannu a taimaki yaran nan domin su sami limi.

Ya ce "mafi yawancin manyan Nijeriya sun yi almajirci saboda haka mu hada kanmu wadanda Allah ya hore mana mu taimaki yaran nan dan ganin sun sami ilimin".

Rochas ya kara da cewa "a gani na yaran nan ba laifin su bane domin Allah ne ya halicce su har suka taso gidan da za a kai su makarantar kuma suke bara don abinda za su ci. Don haka taimaka musu ya kamata a yi ba tarwatsa su ba.

Ya ce "mu manya mu ya dace mu taimake su dan ba mu san wanda zai zama shugaban kasa a cikin su ba. Ina so ku sani karatun Allo da almajiranci musulunci ne ya ce kuma Almajirci ba sunansa bara ba, neman ilimi ne.

1 comment:

  1. Wannan gaskiya ne ya kamata a duba batun wannan mutumin duba da bambanci dake akwai

    ReplyDelete

Pages