Asiri ya tonu: Dan majalisa yayi min fyade, sannan yayi mini alkawarin bani miliyan 20 idan na takura mijina ya sake ni
Wata mata dake zaune tana kasuwanci a jihar Legas ta bayyana yadda dangantakar ta da wani dan majalisa ya sanya ta cikin matsala
- Matar ta bayyana cewa dan majalisar yayi mata fyade, kuma bayan fyaden da yayi mata ya nemi taje ta sanya mijinta ya saketa shi kuma zai bata naira miliyan ashirin
- Yanzu haka dai matar ta bayyana cewa dangantakar dake tsakaninta da dan majalisar ne ya saka aka kama ta aka rufe ta a ofishin 'yan sanda Wata mata 'yar kasuwa mai suna, Nkeiruka Cynthia Kamalu, ta sanar da wata babbar kotu dake jihar Legas cewa wani dan majalisar tarayya mai suna Uju Kingsley Chima, yayi mata fyade a ranar 9 ga watan Agustan shekarar 2015.
Matar ta bayyanawa mai shari'a Nicholas Oweibo cewa bayan dangantakar dake tsakanin ta da dan majalisar yayi mata alkawarin bata naira miliyan ashirin idan ta takura mijinta ya sake ta.
Chima dai shine dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Ohaji/Egbema, Oguta da kuma Oru ta yamma dake jihar Imo. Matar na neman kariya ne daga wajen Chima, wanda ta bayyana cewa ya jawo aka kamata a ranar 27 ga watan Mayun shekarar 2019 dinnan.
Mrs Kamalu ta yi wannan zargin ne a ranar 11 ga watan Satumbar nan da muke ciki. Lauyanta, Chijioke Jiakponna, ya sanarwa da alkali cewa Chima yaki amsa wayarshi, domin duk lokacin da aka kira shi yana katse wayar ne. Alkalin dai ya daga sauraron karar zuwa yau dinnan Talata 23 ga watan Satumba.
A lokacin da jaridar The Nation ta kira Chima a waya akan maganar zargin da ake yi masa, ya daga wayar ya kuma bayyana cewa ba zai iya magana a wannan lokacin ba, da dare yayi aka kara kiranshi sai aka ji wayarshi a kashe.
Legit Hausa
Tuesday, June 2, 2020
Home
Alajabi
Asiri ya tonu: Dan majalisa yayi min fyade, sannan yayi mini alkawarin bani miliyan 20 idan na takura mijina ya sake ni
Asiri ya tonu: Dan majalisa yayi min fyade, sannan yayi mini alkawarin bani miliyan 20 idan na takura mijina ya sake ni
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment