Saturday, May 30, 2020

Buhari Ya Fi Amincewa Da Mata Fiye Da Maza A Mulkinsa, Inji Garba Shehu



Buhari Ya Fi Amincewa Da Mata Fiye Da Maza A Mulkinsa, Inji Garba Shehu

Daga Comr Abba Sani Pantami

Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa shugaban kasa ya fi amincewa da mata fiye da maza.

A yayin zantawa da gidan talabijin din NTA a ranar Juma'a, Shehu ya ce tsarin kudi na gwamnatin Najeriya a halin yanzu yana hannun mata ne.

Kemi Adeosun, wacce ta yi murabus sakamakon shaidar kammala bautar kasa ta bogi da kuma magajiyarta, Zainab Ahmed, sune mata biyu da suka rike ma'aikatar kudi a karkashin gwamnatin Buhari.

A yayin shirin, an tambayi Shehu ko akwai yuwuwar shugaban kasar ya kara wasu mata a cikin gwamnatinsa, wanda Shehu ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar hakan.

Ya kara da cewa, "Ina so ka gane cewa, dukkan ministocinsa na kudi mata ne. "Bari in fadi wani abu, amma ina fatan ba zai saka ni cikin matsala ba, ya fi amincewa da mata fiye da maza .

Dukkan wata amanar kudi a kasar nan, mata yake bai wa kuma suna matukar rike amincin nan. Suna kokari.

No comments:

Post a Comment

Pages