Babu Abunda Buhari Ya Tsinana Tsawon Shekaru Biyar Da Ya Shafe A Kan Mulki, Cewar Jami'iyyar PDP
Daga Comr Abba Sani Pantami
Babbar jami'iyar adawa, PDP, ta ce babu wani abu mai muhimmanci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsinana cikin tsawon shekaru biyar da ya shafe a kan gado na mulki.
Shugaba Buhari wanda ya lashe babban zaben kasa a shekarar 2015, an sake rantsar da shi a wani sabon wa'adi na biyu a ranar 29 ga watan Mayu, 2019.
A wani sako da jam'iyyar PDP ta wallafa a ranar Juma'a kan shafinta na Twitter, ta ce babu abun zo a gani da Buhari zai nuna wa 'yan Najeriya a matsayin bajintar da yayi tun hawansa kujerar mulki.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa, babu abin da ya mamaye wannan gwamnati ta Buhari illa iyaka, miyagun ababe na rashin ci gaba da durkusar da kasar nan.
Cikin sakon da ta rubuta a shafinta, jam'iyyar PDP ta ce shugaba Buhari bai tsinana komai ba face; tsananin rashawa, nauyin bashi, talauci, yunwa, rashin tsaro, kulle da hana zirga-zirga.

No comments:
Post a Comment