
Masana'antar Kannywood ta kai kusan shekara 20 da kafuwa kuma ta samu dinbim jarumai masu taka muhimmin rawa wajen nishadantar da al'umma
A cikin tsawon shekarun da wannan dandalin ta samu asali an samu jarumai mata da dama da suka faranta mana rai da ire-iren rawar da suke takawa a idon telibijin.
Mafi yawancinsu a daina jin duriar su ne kasancewa shiga sahun gaba na rayuwar zamantakewar aure.
Domin martaba da raya wannan dandalin da take nishadantar damu a ko da yaushe bari mu waiwaya baya mu tuna wasu daga cikin tsofin jarumai mata gwarzaye da suka nishadantar damu shekarun baya kafin ire-iren su Hadiza Gabon da Rahama Sadau su amshi tutar raya masana'antar
Ga wasu daga cikinsu
Saima muhammad
Abida muhammad
Fati muhammad
Maijidda Abdulkadir
Maijidda Ibrahim
Aisha Muhammad
Fati Bararoji
Zara'u Shata
Halisa Muhammad
Rahama Sirace
Hafsat Shehu
Hadiza Kabara
Da dai sauransu da dama
Wadannan tare da wasu da dama sun taka rawar gaske yayin da ake damawa dasu a harkar fim kuma sun taimaka wajen inganta al'adar arewa ga bainar jama'a.
Muna musu fatan alheri tare da jinjina masu bisa gudummawar da suka bada a masana'antar kannywood
No comments:
Post a Comment