Friday, February 16, 2018

Yadda Mace Za Ta Kare Kanta Daga Mugun Namiji



Mata, an san su da rauni a cikin al’umma, shi ya sa miyagu suke masu gani-gani a duk lokacin da suka yi arba da su. Filin Hantsi ya yi nazari a kan yadda macen da mugun namiji mai neman cutar da ita ta hanyar sata ko fyade ko wani mugun laifi na daban za ta kare kanta. A karanta cikin tsanaki:

1. Wani mataki mace ya kamata ta dauka idan ta sami kanta a cikin injin hawa bene (lifter) tare da bakon namiji mai neman cutar da ita a cikin daki ko gini cikin dare?
masana sun ce: ta shiga injin hawa bene. Idan tana bukatar ta isa hawa na 13, sai ta danna dukkan maballin har zuwa lambar wurin da za ta sauka. Ba wanda zai iya kai mata hari a kan kowane hawa idan ta yi haka.

2. Abin da ya kamata ki yi idan bako yana kokarin kai miki hari a lokacin da kike cikin gida ke kadai. Ki ruga da gudu zuwa kicin.
Masana sun ce: ke kadai kika san inda aka ajiye yaji. Da kuma inda wuka da farantai suke. Duk wadannan za su iya zama makaman ki ako da yaushe, idan babu su, to fara jifar mugun da faranti da kuma kayan girke-girke ako ina. Barsu su fashe. Karar da wadannan abubuwan za su rinka yi shi ne babban barazana ga mai kawo hari saboda ba ya son a kama shi.

3. Hawa motar haya cikin dare.
Masana sun ce: kafin ki shiga motar haya cikin dare, ki rubuta lambar motar, bayan kin shiga sai ki yi amfani da wayarki ki kira mutanen gida ko kawayenki ki sanar da su cewa kin shiga mota mai lamba ‘kaza da kaza’ kina hanyar zuwa gida (ko inda kike son zuwa). Kar ki manta, ki yi wannan bayanin da harshen da direban zai fahimta. Ko da kin kira ba a amsa ba, ki yi magana kamar an amsa wayar.
Direban zai san cewa wani yana da cikakken bayani a kan shi kuma zai kasance cikin matsala mai tsanani idan wani abu ya faru mara kyau. Yanzu zai dauke ki ya kai ki gida lafiya ba tare da matsala ba. Kin ga a nan, idan direban mugu ne, a maimakon ya cutar da ke zai zama mai kare ki, domin ya san matukar wani abu ya faru da ke, tashi ta kare.

4. Idan kin shiga mota, sai kika ga direba ya juya zuwa titin da bai kamata ya bi ba, kuma kina jin cewa zai kai ki mahallaka ne?
Masana sun ce: ki yi amfani da hannun jakarki ko dankwali ki shake masa wuya. A cikin sakan daya zai ji rauni tare da neman tsayawa. Indan ba ki da jakar hannu ko dankwali, kawai ki ja cakume wuyar rigarsa ki shake ta baya, zai ji kamar numfashinsa zai dauke, dole ya tsaya.

5. Idan dare ya yi maki a wani wurin da kike tsoron fadawa hatsari.

Masana sun ce: ida kika samu kan ki dare ya kama ki, kina kuma tsoron fadawa cikin wani hatsari, kuma gashi shaguna duk sun rufe to ki yi gaggawan neman wurin da aka kafa na’urar ATM, akwai na’urar CCTB da ke daukan hotunan mutane, ki yi bayani kai tsaye a ciki, ko da wani abu ya same ki za a samu bayanin halin da kika shiga ta wannan na’urar ATM din.

Bayan haka, babban makamin kariya ga kowacce mace shi ne kasancewa mai lura da duk hali da muhallin da kika samu kanki, ki kauce wa fita cikin dare ba tare da dan rakiya ba, ki kuma rinka sanya suturar da zai kare maki mutunci a ko da yaushe.

Wadannan su ne kadan daga cikin abin da muka yo maku nazari a kan kariya daga mugun namiji.

No comments:

Post a Comment

Pages