Tuesday, February 6, 2018

‘Ya Ta Kai Karar Mahaifinta Akan Zargin Yi Wa ‘Yar Makota Fyade




An gurfanar da wani direban mota mai shekaru 47 a gaban kuliya a bisa zargin yi wa ‘yar makotan shi mai shekaru 7 fyade.

Asirin mutumin mai suna Adelaja Olaide ya tonu ne bayan da ‘yar shi mai shekaru 17 ta fadawa mahaifiyar yarinyar abunda ya faru.
Mahaifiyar yarinyar ita kuma ta kai kara wajen ‘yan sanda.

‘Yar mutumin mai suna Oriyomi ta fadawa ‘yan sanda yadda mahaifin ta ya sanya ta kira ‘yar makociyar ta su da karyar zai aike ta, amma da ta shiga gidan sai ya tube mata kaya ya yi mata fyade.

Adelede dai ya aikata laifin ne a watan Yunin 2015 a gidan shi da ke yankin Ketu a jahar Lagos, kamar yadda lauyan masu kara Jide Boye ya bayyanawa kotu.

Laifin ya sabawa sashe a 137 na kundin dokar jahar Lagos.

Kotun ta daga sauraran karar zuwa ranar 7 ga watan Fabrilu domin a ji shaidar likitoci.

No comments:

Post a Comment

Pages