Thursday, February 15, 2018

Idan na ba matana Kudi zan mutu, haka al’adan mu yake – Inji magidanci




Wani magidanci Stephen Enebeli ya sanar wa kotun Igando dake jihar Legas cewa lalle zai mutu idan har ya taimaka wa matar sa da kudi.
Enebeli ya bayyana cewa tun da ya yi na’am da umurnin kotu da sun rabu da matarsa da ita da kanta ta shigar ya yanke shawarar daina bata kudi.

Ya ce bisa ga al’adunsu duk namijin da ya taimakawa matar da suka rabu ko kuma tana gidan wani namiji da kudi zai mutu.
” Da yake ban shirya mutuwa ba dole na yanke bata kudin abinci, kudin makarantan yara da sauran su.”

Ya ce yana rokon kotu da ta warware auren su sannan ta damkamasa kula da ‘ya’yan su ganin cewa matar na zaune a gidan wani namiji.

Ita kuwa matar mai suna Eunice ta bayyana a kotu cewa ta shigar da karan mijin ta ya sake ta ne saboda rashin kula da baya bata da barazanar kashe ta da yake yi.

Daga karshe Alkalin kotun Akin Akinniyi ya raba auren ganin cewa matar bata son zaman auren da Enebeli. Sannan ‘ya’yan za su zauna da mahaifiyar su.

No comments:

Post a Comment

Pages