Inalillahi wa Inna ilaihir rajium Manzon Allah s.a.w Yana cewa alamu ne na karshen duniya:
1. Karami ya Rena Babba 2. Babba ya zalumci karami 3. Alfasha da zinace zinace zai yawaita 4. Kunya za ta dauke chak. Alamu sun gama tabbata lalle manzon Allah s.a.w sarkin gaskiya ne.
Duba ga wannan taswirar wata sabuwa fitina ce da ta kunno Kai duniya, kasantuwar cewa ana zinace zinace da Mata ana samun cututtuka wata Rana da ciki da de sauransu ga dawainiya sosai.
Sai kawai technologing mahaukata marasa basira mai amfani ta kawo musu da yin amfani da mutum mutumin mace Dan kore shaawa Wanda haka din babban Zunubi ne Mai yawa. Ina muka dosa, inane makoma, kusani fa Allah shine yayi halitta sannan ya dede ta ta, sannan a gurinsa ne rayuwa da mutuwa take. Sannan a gurinsa ne makoma take sannan shine zai tambaye mu akan abin da muka kasance muna aikatawa.
Wallahi muji tsoron Allah mu Sanja dabiun mu daga munana zuwa kyawawa. Allah ya sauwake. Wannan nasiha ce.
No comments:
Post a Comment