
Biyo bayan ɗan cecekuce tsakankanin jarumai a masan’antar shirin kwaikwayo Kannywood, Fati Abubakar wadda aka fi sani da Fati Shu’uma ta fito ta bayyana iri halaccin da maigida Adam A. Zango ya mata inda tacce shine jagoranta a masana’antar Kannywood, tacce shi ya fara sa ta a shirin kwaikwayo har ta yi suna.
Fati ta kara da cewa kuma abunda Adam ya mata wanda ba zata taɓa mancewa dashi ba shine, lokacin da mahaifiyarta ta rasu, Adam yazo ya zamna tareda mutane aka rinƙa karɓar gaisuwa dashi, tacce wannan abun ba karamin dadi ya mata ba, hatta ‘yan gidansu sunji dadin hakan kuma ba zata taba mancewa dashi ba.
A karshe tace bata ma san da wace irin kalma zata godema Adam A. Zango ba.
No comments:
Post a Comment