Thursday, December 7, 2017

Kuskure Goma Sha daya da akayi a fim din Gida da Waje

Tare Da: Saddika Habib Abba
Suna: Gida Da Waje
Tsara labari: Auwal M Sarki
furodusa: Muhammadu Mia
Bada umarni: Sadik N Mafia
Kamfani: Mia Enterprises
Jarumai: Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Aminu Sharif Momo, Basma Baba Hasin, Sadiya Adam, Baba Karami, Sarki Mukhtar, Sha’awa Adam, Alasan Kwalli da sauransu.
Fim din Gida da Waje labari ne akan wasu ma’aurata Faruk (Ali Nuhu) da Ramlat (Hadiza Gabon) da a ka nuna ba sa jituwa saboda halayyarsu da ba ta zo daya ba domin shi Faruk an nuna mutum ne mai son zuciya mai handama da baba ke re da kudin talakawa a kujerar sa da ya ke ta darakta mai lura da horo da kuma dibar sabbin ma’aikata na hukumar ilimin gaba da primary, sabanin ita matar ta sa wadda kullum ta ke nuna masa cewar abinda yake yi ba dai dai ba ne shi ne dalilin daya ke san ya musu rashin jituwa.
Wannan kujerar ta Faruk da yake yin abinda ya ga da ma na handimar kudin gwamnati tare suke yi shi da wani abokinsa Buhari (Aminu Sharif) a na cikin haka sai wani aminin Faruk (Alasan Kwalli) yaci kujerar gwamna alakarsu da faruk ta san ya ya dauki kujerar kwamishinan ilimi ya ba shi Faruk bai fa sa halinsa ba anan ma yakara samun damar handamar kudin gwamnati ana haka sai kwamitin bincike ta kawo masa takarda akan za ta bincike shi hankalin Faruk ya yi matukar ta shi saboda ya san ba shida gaskiya bayan sun bincike shi suka tabbatar da ya ci kudin gwamnati har naira milyan casa’in da takwas na asusu sannan an sa me shi da badakala ta aringizon dibar ma’ikatan bo gi tare da karbar kudade ba bisa ka’ida ba kwamitin suka umarce shi akan ya dawo da kudin ko kuma su mika shi kotu.
A nan Faruk ya fara cuku cukun yanda zai ga mai girma gwanma amma abu ya gagara ko wayarsa gwamna ya ki amsawa, Faruk yana ta fadi ta shi har Allah yasa ya sami ganin gwamna dakyar, amma duk da haka abinda yakeso bai samu ba don gwamna sai ya nuna masa shi sam gwamnatinsa ba ta cin dukiyar al’umma ba ce saboda haka ko ya dawo da kudin da ake tuhumarsa ko kuma a mika shi kotu, Faruk ya yi kokarin su sami sa sanci shi da abokinsa mai girma gwamna amma abu bai yu ba.
Har sai da kai ya rasa aikinsa kuma an saka masa farar takarda wadda za ta hana shi yin kowanne irin aiki a karkashin gwamnati sannan hukumar ta kwa ce gidansa da fila yensa da motocinsa amma duk da haka sai da aka biyo shi wasu ragowar kudin sakamakon babban aikin da matarsa ta ke yi a matsayinta na manaja a wani babban kamfani ya san ya ta biya wa Faruk wannan ragowar Kudaden sannan ta sai musu gidan da suke ciki a hannun hukumar hakan ta san ya basu bar gidanna su ba suka ci gaba da zama a matsayin mallakinsu.
Wannan dalilin ne ya sa ka Faruk ya koma yin zaman banza na rashin aikin yi dukkan dawainiyarsa data mahaifiyarsa data ‘yarsa Kairat (Basma Baba Hasin) gabaki daya ta koma kan matarsa ita take komai a gidan wannan ma yakara saka musu rashin jituwa a gidan, ana cikin haka wani abokin Faruk ya samar masa aikin masinja a wani kamfani ashe kamfanin da matarsa ta ke aiki ne kuma akayi arashi aka kaishi office din matarsa domin ya zama masinjanta anan Ramla ta yi amfani da wannan damar ta dinga hora Faruk tana ra ma abinda ya ke yima ta a gida suna ta takun sa ka har tai ga a karshe sun sami masalaha saboda barazanar takardar saki da ya yi mata Ramlat taji tsoro saboda kaunar da take yiwa mijinna ta ta dai na duk abinda take yi har ta samar masa Babban office na P.R.O a karkashin kamafin na su.
Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya fito da darasi wanda al’umma za su amfana da shi musamman ma’aikatan gwamnati.
2- Kayan aikin da aka yi amfani da su wurin guda nar da fim din sun kayatar da ma su kallo sosai musamman camera ta daukar hoto da kuma abin daukar sauti.
3- Jaruman fim din sun yi kokari wurin isar da sakon musamman Faruk da Ramlat
4- Guraren da’aka yi amfani dasu gurin daukar shirin sun yi kyau sun kayatar da ma su kallo musamman gida je.
Kurakurai:
1- Akwai in da gwamna ya ke cewa ko ubansa ne Ayuba ya sa ci kudin al’umma sai ya mikashi kotu wannan kalamin kuskure ne ambatar sunan da ya yi domin mahaifi mahaifine babu ladabi aciki bai kamata ya yi wannan misalin ba tunda an nuna jaruman suna kan tafarkin addinin musulunci ne.
2- Akwai lokacin da Ramlat ta ka wo wa Faruk kudin albashinsa bata fada masa ko nawa bane ya ke tambayarta ya zai ga dubu bakwai ina ragowar? ta yaya yasan dubu bakwai ne tinda ko irga su bai yi ba, kallon su kawai ya yi kuma anin ke suke kudin.
3- An nuna Buhari tare suke aringizon kudi da Faruk kuma an ga karshan Faruk amma ba’a nuna karshan Buhari ba hasali ma sai ribar wankeshi da Faruk ya yi a kotu yakamata aga karshan Buhari saboda darasi.
4- A lokacin da Faruk ya shigo office din manajan kamfanin da ya sami aikin masinja ya tarar cewar matarsa ce manajan mamaki ya bayyana a fuskarsa itama Ramlat yakamata aga mamaki a fuskarta, ganin shigowar Faruk office din a matsayin masinjanta tinda bata ma san yana neman aikin ba, kawai ganin sa ta yi amma sai ga shi ramlat ta da ke tana magana cikin isa tamkar da ma can ta san da zuwansa.
5- wurin da aka nuno Faruk da gwamna suna tatttaunawa bai kamata ba aga gwamna a wannan wurin, domin yakamata a ce an gansu ne a zaune a falo ko kuma wani guri na alfarma amma sai ga su a saman bene a tsaye a wata karamar baranda su biyu rak ko masu tsaran gwamna babu sannan babu wata alama da za ta nuna cewar gidan gwamnati ne.
6-Akwai in da ake nuno Ramlat babu mayafi a jikinta ta saka doguwar riga mayafin doguwar rigar shine ta daura akan ta a matsayin dankwali kuma aiki za ta fita a matsayinta na matar aure bai kamata ace an gan ta a haka ba.
7- Daraja da kima irin ta aure a ko’ina namiji yana sama da matarsa ita aka ce tayi masa biyyaya a duk in da ta tsinci kan ta duk mukaminta yana sama da ita amma irin abubuwan da Ramlat ta dinga yi wa Faruk na kaskanci a office ya sa ba da koyarwar musulunci.
8- akwai in da Ramlat ta ke tambayar babar mijinta har yanzu mutuniyarta Balaraba ba ta da wo ba ne? ai gwara ta da wo domin ta yi kewarta sosai amma kuma abin mamaki sai ga shi haduwarsu ta farko lokacin da Balaraba ta ka wo mata ziyara gidanta ko magana Ramlat ba ta yi wa Balaraba ba rashin mutunci ma da ta bita dashi, ina kewar ta ta data ce tana yi?
9- tsarin tarbiyyar bahaushe ba’a magana wadda bata kamata ba a gaban yara kanana saboda tarbiyyarsu amma a fim din sai ga shi akwai wuraren da Faruk da Ramlat suke rigima suna fadin abubuwan da basu kamata ba a gaban Kairat itama Kairat din tana rarraba idonu tana binsu da kallo, akwai ma in da Ramlat ta ke baiwa mahaifiyar Faruk labarin laifukan da ya yiwa gwamnati duk a gaban kairat hakan bai kamata ba, kamata yayi ace an samar da dalilin da Kairat ba ta wajan ko da makaranta ce ace tana can.
10- An nuna Faruk mutum mai son fantamawa da nuna shi wani ne harma akwai in da yake cewar matarsa so ya ke yi idan ta jero da matar gwamna aka sa bam bam ce su amma sai ga shi a karshe yana cewa matarsa Ramlat shi mutum ne ba mai karya ba yana daukar rayuwarsa dai dai ruwa dai dai tsaki shiyasa ya ke hawa tsohon mashin bayan an nuna Faruk a waccen halayyar.
11- Ba bu yanda za’ayi miji ya kawo wa matarsa takarda wacce take kyakyawan zargin ta sa ki ce amma kuma taki budewa ta karanta saboda kawai bata san me za ta ce a gida ba idan sakin ta akayi, kuma ta cigaba da zaman aure da mijin har ta dinga jin haushin kaurace mata da ya yi, shin Ramlat batasan ka’idar musulunci ba ne? kuma aka nuna ta a matsayin ita mai kiyaye dokokin ubangiji ce har tana nusar da mijinta, shin idan da ace ta tabbata sakin ta Faruk ya yi wannan zaman da ta yi da shi a wana matsayi ta ke a gurin Allah?

No comments:

Post a Comment

Pages