Saturday, November 18, 2017

Yadda Aka Kafa Kofofin Zazzau Tun Kafin Karne Na 17



Tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka kasar Hausa, manyan dadaddun garuruwan yankin sun kasance suna da wani gini mai tsawo da ake zagaye su da shi da aka yi wa lakabi da ganuwa. A wannan ganuwar akan yi wani tsari mai kyau na bude kofofi a wasu muhimman wurare domin shigowa ko fita daga gari.
Ko wace kofa da ake yi ana rada mata suna a sakamakon wata munasaba. Ire-iren wadannan sunaye da ake rada wa kofofin manyan garuruwan sun shafe shekaru aru-aru a cikin tarihi ba tare da sauyawa ba duk da cewa sun fuskanci juyin cigaba na zamuna daban-daban. Har ila yau, sunayen kofofin garuruwan saboda kaifin hikima da basirar ta al’ummar dauri, sukan sha bamban da takwarorinsu na sauran garururuwa.
A cigaba da nazarin waDannan kofofi na tarihi a Kasar Hausa, LEADERSHIP A Yau Juma’a ta leka Birnin Zazzau domin nazarin kofofinta na asali wanda nazari ya tabbatar da cewa masana tarihi sun baje hajar kolin fasaharsu kan kofofin, kamar yadda bayanan da muka samu daga fitaccen marubucin tarihin nan a Lardin Zazzau, Sarkin Ayyukan Zazzau, Malam Abbas Mohammed Fagachi suka nunar.
A rubuce-rubucensu, masana tarihin sun bayyana cewar bayan an kammala ginin ganuwar da ta zagaye Birnin Zariya tun da farko, an samar da kofofi takwas da suka zama kofofin da ta cikinsu ne kawai ake shiga tsohon garin. Kuma an yi abubuwa biyun ne, wato Ganuwa da Kofofin domin kare babban birnin na Zariya daga hare-haren mayakan sauran masarautu na dauri.
Kofofi shida da aka fara sara tun kafin karne na 17 su ne: Kofar Gayan, Kofar Kuyan Bana, Kofar Tukur-Tukur, Kofar Doka, Kofar Bai, da Kofar Kona. Masana tarihi sun yi bayanin cewa ko wace kofa tana da sunan da aka rada mata bisa wani dalili ko munasaba.
Kofar Gayan: An samar da wannan kofa ce domin sada Birnin Zariya da tsohon garin Turunku, kuma an sami wannan suna ne daga sunan wani rafi da ake kira ‘Gayan’ da a yau yake Karamar Hukumar Igabi. A wajen da wannan kogi yake, akwai wani gari da ake kira Gadar Gayan.
Kofar Kuyan Bana: A tarihin kofofin da suke Zariya, wannan ita ce ta biyu da aka samar cikin kofofin da suka zagaye Birnin Zariya. Kuma masana tarihi a rubuce-rubucen da suka yi, sun bayyana cewar wannan kofa, an sa ma ta wannan suna na Kofar Kuyan Bana ne daga sunan wani babban mayakin Sarauniya Amina.
Shi wannan mayaki Kuyan Bana, fitaccen jarumi ne domin shi ne aka tabbatar da ya zama jagora wajen samar da wani gari da ake kira Kuyan Bana wanda a yau wannan gari yana kudancin garin Kwatarkwashi. Har ila yau, kasancewar ya gina gidansa kusa da wannan kofa da aka sa sunansa, sai kuma Sarauniya Amina ta bashi gadin kofar.
Kofar Kona: Wannan kofa an tabbatar ita ce kofa ta uku da aka samar a ganuwar Birnin Zariya. An tabbatar da cewa an sa wa wannan kofa wannan suna ne daga sunan wasu masana ilimi da suka kasance a Zariya a karni na goma sha biyar wadanda a lokacin da suka fara zuwa Zariya, sun yi zango a gefen garin, to da aka sara wannan kofa da ke kusa da inda suka share suka zauna, sai aka sa wa wannan kofa sunan Kofar Konawa, amma da tafiya ta ta yi tafiya,sai aka fara kiran kofar da sunan Kofar Kona kawai, inda abin ya cigaba har zuwa wannan rana. Bayan malaman sun shafe ‘yan shekaru suna zama a gefen Kofar Kona, sai suka bar wajen suka koma inda suke a yau wanda kuma ake kira da sunan Limancin Kona. An tabbatar da cewar a dalilin waDannan masana ilimin addinin musulunci ne aka sami wannan suna na Kofar Kona.
Kofar Tukur-Tukur: Wannan kofa, ita ma masana tarihi sun ce, kofa ce da ta zama kofar da al’ummomin garuruwan Gobir da wani gari da ake kira da suna Kabi da a yau aka fi sani da Birnin Kebbi da Yawuri da Zamfara ko kuma Zamfarawa ke shiga cikin Zariya. Kuma an sami sunan wannan kofa ne daga wani Dutse da ke garin Tukur-Tukur. Wannan gari na Tukur-Tukur, an ce yana cikin tsofaffin garuruwa da suke Lardin Zazzau. Amma saboda yake-yaken da su ka yi ta faruwa a wancan lokaci, a zamanin Sarkin Zazzau Sambo da wanda ke jagorantar garin Ningi Haruna, sai aka canza sunan wannan kofa zuwa Kofar Kibau. Wato kofar da kibau ke wulkawa saboda yake-yaken da ake yi a wancen lokaci, wanda har zuwa yau da kibau Din suka daina wulkawa an cigaba da kiran kofar da sunan Kofar Kibo a maimakon sunanta na asali, wato Kofar Tukur-Tukur.
Kofar Doka: Wannan kofa ita ce kofa ta biyar da aka sara a Ganuwar Zariya. Da farko wannan kofa ana kiranta da sunan Kofar Kano. Masana tarihi sun ce an sa wa wannan kofa wannan suna ne daga wata itaciyar Doka da ta ke kusa da inda aka sari kofar. Sai dai kuma, an sami wani bayani na tarihi da ya ce sunan jarumin da ke gadin kofar ne Doka, sai aka rika kiranta da sunansa, daga nan sunan ya zauna har zuwa yau.
Har ila yau, wasu masana tarihi sun ce itacen Dokar da aka saw a kofar, tana cikin gidan Sarkin Zazzau Alhaji Abubakar Dan Malam Musa a unguwar Kofar Doka, wanda a yau a wannan gida ne mazaunin gidan Yari yake.
Kuma masana tarihi sun ce ta wannan kofar ce al’ummomin garuruwan Kano da Katsina ke shiga Birnin Zariya.
Kofar Bai: Masana tarihi sun ce an sa wa wannan kofa wannan suna ne a dalilin inda aka sari kofar na bayan gidan Sarkin Zazzau, wato kofar bayan gidan Sarki, amma a takaice sai ana kiran kofar da sunan Kofar Bai. Ita ma wannan kofa ita ce kofar da al’ummar Bauchi ke shiga Birnin Zariya. Masana tarihi sun nuar da cewar kofofin da aka ambata su ne kofofi na farko da aka sara su tun farkon tarihin Birnin Zariya.
Bayan waDannan kofofin guda shida da aka fara samarwa, a Karni na goma sha bakwai Masarautar Zazzau ta samar da karin wasu kofofi biyu da suka hada da:
Kofar Jatau da kuma Kofar Galadima. Su ma ga bayanansu kamar haka:
Kofar Jatau: Masana tarihi sun ce an rada wa wannan kofa sunan wani Sarki ne a mulkin Habe mai suna Isiyaku Jatau, wanda ya ja silin mulkin Zazzau daga shekara ta 1782 zuwa shekara ta 1802.
Wasu bayanai kuma sun ce sunan wani mayaki ne mai gadin kofar Jatau da aka sa kuma hakan ya faru ne a zamanin Sarkin Zazzau Jatau. Kofar Galadima: Wannan kofa, masana tarihi sun ce an sa mata sunan Galadiman Zazzau Daudu ne.
Shi Galadima marokan fadar Sarkin Zazzau na yi ma sa kirari da “Galadima, Daudu rana da hazo kofar birni”, wato abin nufi shi ne shi mutum ne da ako wane lokaci hannunsa a budde ya ke ga marokan fadar. Wasu masana tarihi kuma sun bayyana cewar, an sa wa wannan kofa sunan Galadima Dokaje ne.
A duk zantukan nan biyu waDanda suka yi karo da juna, an dai yanke hukuncin sunan wannan kofa dai Kofar Galadima. A cewar masana tarihin, an sa wa kofar sunan Galadima ne kasancewar gidansa na kusa da inda kofar ta ke.
A lokacin Gwamnan Jihar Kaduna a karkashin gwamnatin Soja, Kanar Lawal Jafaru Isa da ta farar hula a karkashin Alhaji Ahmed Miohammed Makarfi, gwamnatin jihar ta gyara wasu
daga ckin kofofi da aka ambata. Kofofin da gwamnatin ta gyara su ta mayar da su na zamani su haDa da, Kofar Doka, Kofar Kibo, Kofar Jatau, Kofar Kuyan Bana, da kuma Kofar Gayan, sai kuma Kofar Kona da gwamnatin ta fara gyarawa amma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton ba a kammala ba.
LEADERSHIP A Yau Juma’a ta samu damar zantawa da Sarkin Kofar Zazzau, Alhaji Mansur Dambo Mai-Sa’a inda ya yi mana karin haske kan batutuwan da suka shafi kofofin.
Ya fara da bayyana tarihin sarautar Sarkin Kofa a fadar Zazzzau.
“Babu shakka a da akwai abubuwan da aka fadi na masu gadin ko wace kofa, kuma ko wace kofa tana da Sarkinta amma daga baya mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ya naDa Sarkin Kofa na farko wanda aka nada mahaifina, marigayi Alhaji Dambo Maisa’a. Bayan mahaifina ya rasu sai aka naDa ni Sarkin Kofan Zazzau, wato duk wasu al’amurra na kofofin sai aka mayar da su a karkashin Sarkin Kofan Zazzau”.
A tarihin kofofin dai, a baya ko wace kofa tana da makullin da ake rufe ta amma a yanzu babu alamar haka. Sarkin Kofa ya bayyana dalili.
“Kamar yadda kila ka sani muhimmancin kofofin su ne kare Birnin Zariya daga masu kai hari a garin, tun da ka san a waDancan shekaru akwai yake-yake a tsakanin garuruwa, ka ga yanzu za a iya cewar ana zaune lafiya, shi ya sa babu masu gadin kofofin, ba a kuma rufe kofofin da suke Zariya. Kuma rufe kofofin a ko wane lokaci kan ba sarakuna da sauran shugabannin
al’umma su san masu shiga garin da kuma ma su fita garin. In ka lura, yanzu ga hanyoyin shiga Zariyar nan ko ta ina, ba lallai sai ta kofofin da aka zano sub a, a dalilin haka zan iya cewar,babu wasu tsare-tsare na kula da waDannan kofofi a yau.
“Za ka yadda da ni cewar, mutum zai shiga gari ba tare da Sarkin kofa ya san ya shiga ba, haka ma fitar, za a fita bai san an fita ba, amma a wancan lokaci wanda ya shiga an san ya shiga, haka ma wanda ya fita Sarkin Kofa ya san ya fita. Rashin ka’idodin da na ambata suka sa a yau matsalolin tsaro suka yi yawa na yadda al’umma na shiga gari a duk lokacin da suka ga dama, su kuma gina a duk inda suka ga dama. Bacewar wadannan tsare-tsare sun haifar da kamfar tsaro da kuma fitinu daban-daban a tsakanin al’umma da wasu da ba ‘yan kasa ba suke haddasawa ba a Zariya kawai ba; a sassan Nijeriya baki Daya”.
An tambaye shi, da yake muhimmancin kofofin ba za su misaltu ba, ko zai yiwu a kwatanta dawo da yadda aka rika kula da su a baya? Ya amsa da cewa, “Wannan wani al’amari ne na Allah, in zai yiwu shi kaDai ya sani, in ya ga dama zai iya dawo da wancan tsari ta hanyar zamani da za a yi kwaskwarima ga wannan tsari da za su yi dai-dai da zamanin da muke ciki ni da kuma kai. Kuma in aka sami tsaro a duk inda Ganuwa ko Badala ta ke, in an farfaDo da su an kuma gyara kofofin, babu shakka za a sami tsaron da hukuma ke bukata. Dangane da batun mayar da kofofin irin na zamani da wasu Gwamnatocin Jihar Kaduna na baya suka fara ba a kammala ba kuwa, Alhaji Mansur Dambo ya shawarci gwamnatin jihar mai ci ta kammala aikin domin janyo hankalin masu yawon buDe ido.
“Haka ne, an gyara wasu kofofi kamar yadda ka bayyana amma fa masarautar ba sau Daya ba ta yi hobbasa wajen ganin Gwamnatin Jihar Kaduna ta ci gaba da gyara kofofin al’amarin ya faskara, musamman ma Kofar Kona da aka fara gyarawa aikin ya tsaya.
Kamar yadda ake girmama al’adun gargajiya, waDannan kofofi na cikin wuraren da ya dace gwamnatin jihar ta gyara domin in an ziyarci Jihar Kaduna daga wasu kasashe, waDannan kofofi su shiga cikin wuraren da za a ziyarta”.
Ya lissafa muhimman wuraren da ya kamata a mayar da hankali a kai wurin gyarar, inda ya ce “ai kofofin suna da yawa kamar Kofar Gayan da aka gyara tana bukatar gyara. Haka ma Kofar Kuyan Bana, akwai wasu wurare a kofar da suke bukatar gyara, a gaskiya dukkanin kofofin suna bukatar gyara fiye da yadda kake tunani”.
Kofofin na Birnin Zazzau dai sun kasance muhimman wuraren tarihi da masu nazarin tarihi ke cigaba da zakulo al’amuran da suka shafe su walau kafin kafa ko lokacin kafa su ko bayan nan wanda Dalibai musamman na fannin tarihi a jami’o’i ke cigaba da amfanuwa da su.
Karshen tattaunawarmu da Sarkin Kofan Zazzau Alhaji Mansur Dambo Mai Sa’a ke nan,Godiya ta musamman ga fitaccen marubucin tarihin nan a lardin Zazzau,wato Sarkin Ayyukan Zazzau,Malam Abbas Mohammed Fagachi,da ya bayar da gudunmuwa mai yawa wajen tarihin kofofin Zariya,Allah ya ci gaba da yi ma na jagora,amin.

No comments:

Post a Comment

Pages