Saturday, November 18, 2017

Fitattun Mawakan Ingausa(Hiphop) Guda 10



Nomisgee
Aminu Abba wanda aka fi sa ni da Nomisgee, daya daga cikin jiga jigan manya ma waka dake yi ma Arewa hidima, haifafen garin Kano ne. Mutun na farko da ya fara kirkiran dandali musamman don mawakan Arewa matasa masu tasowa, kuma mawaki Hip Hop na zamani. Wakokin sa cike suke da isar da sako, wa’azantarwa, ilmantarwa, Musamman ga matasa. Kuma Ambassador ne Arewa Hip Hop. Yana daya daga cikin ma wakan da Arewa ke alfahari dasu, musamman in ka yi duba da irin kokarin da ya yi gurin sa ma matasa sha’awar wakar hip hop da kuma wayar da kan al’umma baki daya. Ya yi karatunsa a Bayero Unibersity da ke Kano, daya daga cikin wakokinsa dake tashe akwai “Young ALhaji”.
Classik
Buba Barnabas wanda aka fi sa ni da Classik, mawakin mai cika da salo da kyalkyale a wakokinsa na hausa Hiphop. Classik dan a salin garin Bauchi, ya kuma taso ne a Kano, in da yayi karatunsa sa’a Bayero Unibersity of Kano, ya karanci Computer Science, daga bisa ni kuma ya koma Jos dan cigaba da harkokinsa na waka. Yana aiki ne tare da kungiyar “Finese Entertainment” wanda suke masa lakabi da Arewa mafiya, su kan kira kungiyar Play House. Sunansa na gayu yayi dai dai da salon shin a waka, dan kuwa shi ya kanyi wakokinsa sa ne da salo daban daban, zan iya ciwa a mawakan nijeriya baki daya zai yi wuya a samu ma waki mi salonsa. Classik shine matashi na farko da ya fara waka da kananan shekaru a wancan Lokacin, don rahotannin sun nuna ya fara waka tin yana dan shekara 16, ya samu karbuwa kwarai a mutanan Legas. Cikin kwanakin nan yayi bidiyon waka da fitacciyar jarumar Kannywood Rahma sadau, mai taken “I Lobe U”. daya daga cikin wakokinsa da suka yi suna itace “Duniya”
BOC Madaki
Lukas Bulus Madaki wanda aka fi sani da BOC, Barde Ogan Chasu, haifaffen Jihar Bauchi. Ma waki ne da kan iya waka da harshe biyu da hausa kuma yayi da Turanci. Ma goya bayansa na kara hauhawa, amma hakan bai sa ya dau giriman kai yasa ma kansa ba balle ya manta usilinsa. Ma wakine da yake abubuwan sha’awa a Arewa, Musamman yanayin shigarsa. Da daman sun yarda gwani ne shi a fagen sana’arsa. Daya daga cikin wakokin sa da sukayi fice shine Zafi, wanda ya yi shi a cikin album dinsa na no English.
DJ Abba
Cikakken sunansa Abba, Allah ya bashi baiwar abubuwa guda biyu a fiskan sana’ar su. Ma waki ne kuma yakan dau nauyi shirya wakoki. Yana iya rapping da harshen hausa da na turanci baki daya. Fitaccen mawaki ne na hip hop kuma Haifaffen garin Kaduna. Yana aiki ne a karkashin kungiyar yaran North Side (YNS) kuma yana da studio na kanshi mai suna YNS Studio a Kaduna, Yana daya daga cikin manya kuma sanannun mawaka a Arewancin Nijeriya. Salon shi na waka ne yake birge al’umma, kuma yana taimaka masa gurin haska tauraruwarsa. Daya daga cikin wakokinsa da ya fi so shi ne Babarsa.
Morell
Musa wanda aka fi sa ni da Morell haifaffen jihar Borno, yana daya daga cikin ma wakan da suka fara kawo wakar hip hop arewa, yakan yi wakokinsa ne da salo biyu, yayi Hip hop kana kuma yayi bakin Ganga, a wannan lokacin yana daya daga cikin ma wakan da tauraruwar su ke haskawa.
Mutun ne mai saukin kai da hulda da mutane, murya baiwa ce wanda Allah ya bashi dan kuwa zan iya cewa a mawakan mu na yanzu yana da wuyan gaske a samu mawaki mai murya kamar shi.
Morel ya na aiki ne yanzu a karkashen dungiyar Nordan Orty Entertainment, kuna nasan kowa na sha’awar sauraran wakarsa ganga da garaya. In da yayi kokarin girmama harshen hausa bisa da na turanci, yayi karatu ne a Unibersity na Maiduguri. Daya daga cikn wakokinsa da suka daga shi akwai “Anti Social” wanda suka yi tare da sanannen mawakin Duniya baki daya Olamide.
Hafeez
Hafeez matashin mawaki mai dinbin basira a fannin hip hop na arewa. Hafeez haifaffen garin Kaduna ne, kuma ya taso ne a cikin Hausawa tsantsa wanda ya taimaka masa gurin Magana da harshen Hausa.
Yakanyi aikinsa ne da kwazo kuma yana mai da hankali kwarai musamman in yana waka, Kuma yana samu ci gaba a sana’arsa, tare da goyan bayan al’umma baki daya. Shi da kanshi yankan yi ma kansa kirari da “King of the north” Ko kuma yace “Sarkin Sautin Arewa”, yayi wakoki da dama da manyan ma waka a Nijeriya, kamar Dabido wanda suka yi wakar “Taka rawa” tare.
Dezell
Ibrahim wanda aka fi sa ni da Dezell, Allah ya bashi basira da hazaka da kaifin hankali da harshe mai iya fidda kalamai masu shiga jiki.
Haifaffen garin Kano ne, yayi karatunsa a kasar waje. A can ya fara harkansa ta waka da bisani kuma ya dawo kasar sa nijeriya, kuma Arewa dan ya ci gaba da har kansa na waka da harshen hausa. Shine ma waki na farko da ya fara hada kan ma wakan arewa guri guda sukayi waka tare, mai taken “BA BU RUWANMU DA HATER”, wanda ya hada da Morell, BOC, Khengz, Dj Ab, Classik dashi kansa.
Daya daga cikin wakokinsa dake tashe yanzu haka, itace “Aisha” wanda su kayi tare Da sanannan Matashin ma wakin Nijeriya, Koredo Bello.
Kheengz
Khengz wanda aka fi sani da YFK, mawaki na farko arewa dakan iya waka da harshe har guda 3 yayi da Turanci da Nupanci kuma yayi da Hausa.
Shi ne a sahun gaba na ma waka dake tashe a Minna baki dayan yankin Niger State. Ya kamala karatunsa ne a Unibersity of Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ya kuma karanta Civil Engineering.
Ya shahara da murya mai amo, da taushin sauti a wakokinsa.
Ayyukansa a koda yaushe a saukake suke, Kheengz na daya daga cikin mawakan da ke daga darajarta Arewa a duniyar wakokin zamani a Nijeriya.
Daya daga cikin wakokinsa da suke tashe akwai “KEWA”.
Dr. Smith
Simon Bulus wanda aka fi sa ni da Dr. Smith, haifaffen Garin Plateau a karkashin Pankshin Local Gorbernment.
Yana mai da hankali gurin ganin wakokinsa sun fita tsaf, in da al’umma da dama suna mai kirari da likitan hip hop. Shahararren mawaki ne da yake da masoya a Arewa musamman ma a Jos.
Ba’a harkan wakokin hip hop na hausa ba kadai ya tsayaba, yana kuma aiki da gidan rediyon Unity FM da ke Jihar Plateau.
D Dough
Dough matashin mawaki mai dinbin basira a fannin hip hop na Arewa. Mawakin haifaffen garin Kaduna ne, kuma ya taso ne da burin zama mawaki a rayuwarsa.
Ya kanyi aikinsa ne da kwazo kuma yana mai da hankali kwarai musamman in yana waka, Kuma yana samu ci gaba a sanaarsa, tare da goyan bayan alumma baki daya.
Shi da kanshi yankan yi ma kansa kirari da “Abokina”, yayi wakoki da dama wasu daga cikin wakokinsa akwai kamarsu Abokina, Illuminati, da kuma yallabai wanda sukayi tare da Claasiq.

No comments:

Post a Comment

Pages