Hukumar yan sanda a jihar nija ta kama wani magidanci Likita Manu mai shekaru 40 wanda ya kashe mahaifiyar sa kan zargin kashe mai diyar ta hanyar tsubbu.
Jaridar punch ta kawo rahoto cewa an kama Manu tare da mahaifn sa Kwacha mai shekaru 80 wanda ya taimaka masa wajen dukan mahaifiyar har numfashin ta ya dauke.
Labari ya nuna cewa manu ya hau mahaifiyar shi da duka bisa ga zargin kashe mai diya ta hanyar tsubbu.
Shima mahaifin sa Kwacha ya taimaka mai wajen aikata laifin wanda yayi sanadiyar mutuwar matarsa. An kama su ne bayan karar da makwabta suka kai ga rundanar yan sanda.
yayin da yake bada amsar tambayoyi a ofishin yan sanda mahaifin ya shaida cewa yarinyarb itace mutum na tara da matarsa Kaiyo ta kashe ta hanyar tsubbu kuma ba wai yayi niyan kashe ta ba, lamarin ya faru ne bayan ya nemi ya dan zane ta da icce bisa ga abun da tayi da jikan sa wanda ya fusatar dashi. Da aka tambeyi shi ta yaya ya gano cewa mahaifiyar shi ta kashe diyar shi Manu yace: "Mun gano ta hanyar diyata Magajiya yayin da take jinyar wata rashin lafiya. Tana ta kuka tare da rokon kakar ta Inne Kaiyo da ta saki ruhin ta.
Muma mun roke ta amma taki amincewa. kuma ina sane cewa mahaifiya ta mayya ce." Jami'in hulda da jama'a na rundunar Asp Abigail Adaeze ta tabbatar da lamarin kuma tace za'a gurfanar dasu gaban kotu bayan an gama bincike akan su.
No comments:
Post a Comment