Sunday, November 19, 2017

Takaitaccen tarihin Ahmadu Bello Sardauna



An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan Yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya.
Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.

KARANTA:- Yadda mukeyi da kudinda muka karbo daga Barayin gwamnati-Gwamnatin nigeria


Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.
Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.
A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.

KARANTA:- Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala

KARANTA:- Jam'iyyar APC Ba Ta Cancanci Zama jam'iyya Ba — Inji Buba Galadima

KARANTA:- Yadda momo ya kunyata umma shehu a wata hira da sukayi


Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948. Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.
Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966. Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun 'yancin kai.
Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.
Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.
An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.

No comments:

Post a Comment

Pages