Sunday, November 19, 2017

EFCC Ta Gargadi Anyim Kan Kudaden Da Ya Karba Hannun Dasuki



Hukumar EFCC ta gargadi Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Pius Anyin Pius kan ya gaggauta maido da Naira milyan 520 daga hannun tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki. A cikin makon da ya gabata ne, aka rika yayata rahoton cewa EFCC ta cafke tsohon Sakataren gwamnatin Tarayyar bisa zargin rashawa. Kakakin EFCC ya nuna cewa za a bayar da wa'adi ga Anyi din don ganin ya maido da kudaden cikin mutunci.

No comments:

Post a Comment

Pages