Tuesday, November 14, 2017

MARTANI ZUWA GA GARBA SHEHU, HARBI GA DAN JAKI GADO NE



Daga Mansur Ahmed jaridar Rariya
Ba laifi idan mutum kamar Garba Shehu da PDP ta yiwa riga a matsayin mai magana da yawun Atiku yau a wayi gari yana zagi ko cin zarafin ta, ko wani na ta tunda a Shekarar 1999 - 2007 Babu wani cin zarafi ko magana mai zafi ko muni da Garba Shehu zai fad'awa wani mutum a duniyar nan wadda bai fad'awa Muhammadu Buhari ba a lokacin da yake ofishin Atiku a matsayin S.A. da kuma lokacin da suke AC da ACN, wannan ya nuna shi a matsayin mutumin da zai iya kasancewa tare da kowa, domin Buhari shine ne misali Mutumin da bai ji kunyar fad'awa yan Nigeria cewar b'era ya hana shugaban kasa shiga ofishin sa ba ofishin da mutunci, daraja da kima a kasar nan ba ko ofishin Shugaban karamar hukumar mu bai kamata a fadi haka akan sa ba. Garba Shehu da shekaru basu hana shi yi wa talakawan kasar nan karya a lokacin da Buhari yake jinya cewar yana nan a cikin koshin lafiya ba, sai shi kuma Buhari a lokacin daya dawo ya bayyanawa yan jaridun kasar nan a Villa cewar bai tab'a yin rashin lafiya kamar ta wannan lokacin ba a tarihin rayuwar sa tunda aka haife shi. Farfesa Itse Sagay yace jam'iyya mai mulki ta APC jam'iyyar masu cin hanci, rashawa ce da b'arayi wadda yana cikin mashawartan shugaban kasa, wannan ba shine zai nuna maka karshen kunya ta Nigeria a Idon duniya ba?? Kayi magana akan mutumin da ake tuhuma da laifi bai kamata ya fito yana zagayawa da sunan neman takarar shugabancin kasar nan ba hakan yana kunyata kasar nan a idon duniya, El-Rufai ya tab'a fadawa duniya cewar Atiku b'arawo ne haka Obasanjo yayi magana akan Atiku b'arawo ne kuma babu wadda har yau ya musa haka a matsayin ka na mai magana da yawun sa a lokacin kace a hukunta shi? kuma yana takarar shuganancin kasa shi bai kunyata kasar ba? Mantuwar da kayi Garba shine a gwamnatin Buhari a ma'aikatar da yake ministan mai aka saka hannu a kudin da tunda ake a kasar nan ba'a taba sa hannu akan kudi irinsa ba kuma karamin ministan mai na kasa Kachiku ya bayyana lamarin amma me aka yi akan haka zuwa yau? Kudin MTN naira miliyan dari biyar da aka tuhumi Abba kyari dashi ina maganar ta kwana??, batun Maina yana yawo a kasa Ina batun Mainonin da suka dawo da Maina aiki bayan Jonathan ya kore shi?? Me ya dawo da Dambazau bayan Jonathan ya kore shi akan laifi? Mutum a kasa irin Babachir a same shi da almundahanar kudi duk bai kai a kunyata kasa a idon duniya ba?? Batun Shari'a da ka yi Sule Lamido yana matsayin mutum mai bin doka da odar kotu zuwa yau ya halarci zama da aka gudanar sau 26 kuma ko ranar laraba mai zuwa zai je shi Kotu, maganar yana matsayin mai laifi kuma wannan hakkin kotu ne to amma tunda har kayi masa hukunci akan haka har kana tab'a iyalan sa wannan babu laifi, tunda gashi har kana yiwa jam'iyyar PDP da ya'yanta da ita ta haife ka, wadda badan ita ba da babu kai a wajen da kake kai yanzu Ya kamata Garba ya bawa mai gidan sa na wucin gadi Buhari shawarar yana bin umarnin kotu kamar yadda Sule Lamido yake bi, ta kai har kotun ECOWAS na bada umarni akan a saki Sambo Dasuki amma mai gidan ka bai yi biyayya a umarnin kotunan ba, wannan bai kai kunyata kasa a idon duniya ba?? bayan mutane da suke gasu nan ana ta kamawa da laifin kudi a Gwamnatin Buhari amma an kasa fitowa a gurfanar dasu ko kotu ta hukunta su Idan zargin aikata laifi ne yake sawa ayi wa mutum hukunci babu laifi muje zuwa gaba kad'an gaskiya zata bayyana kanta, tunda Garba Shehu bai san mutanen Kano suna zargin yana sayen gidajen mutane a Hotoro bayan gidan Aminu Wali ba, wata rana allura zata bayyana garma Sule Lamido yana goyon bayan yak'i da cin hanci da rashawa da gwamnati take yi matuk'ar za'a hukunta kowa kuma za'a gurfanar da duk wadda ake tuhuma a cikin APC ko Gwamnati duk girman muk'aminsa ko kusancin sa da shugaban kasa. Idan zaku fito ku yiwa talakawan kasar nan aiki ku fito lokacin kushe wani ko musguna masa ko yarfe, k'aharu, k'azafi ko barazana ya wuce talakawa sun dawo daga rakiyar APC domin sun gane babu komai a cikinta sai k'arya da yaudara, Hangen nasarar da takarar Sule Lamido take samu ya saka hankalin ku tashi to Insha Allahu sai ya karb'i kasar nan a 2019. Mansur Ahmed Ya rubuta daga gidan siyasar Sule Lamido 12/11/2017

No comments:

Post a Comment

Pages