Shugaba Muhammad Buhari ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai a wani Masallaci da ke garin Mubi a jihar Adamawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50.
Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a kan harin inda ya kalubalanci mutanen yankin Arewa maso Gabas kan su sanya ido tare da kai rahoton duk wanda ba su amince da shi ba.
Haka ma, Shugaba Buhari ya umarci Sufeto Janar na 'yan sanda kan ya gaggauta kara tura jami'an 'yan sanda zuwa jihar Zamfara don kawo karshen kashe kashe da 'yan Fashi ke yi a kan wasu kauyaku na jihar.
No comments:
Post a Comment