Wednesday, November 22, 2017

An kama matar da ake zargi ta soki mijinta da kwalba a kirji



Kwana hudu bayan wata mata a Abuja ta caccaka wa mijinta wuka, an kuma samun wata da ta caka wa nata mijin kwalba a Gusau babban birnin jihar Zamfara, har ta kai an garzaya da shi asibiti ranga-ranga.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara dai ta ce tuni aka kama wadda ake zargin.
Dan'uwan mijin, Yusuf Abubakar Maga-yakin Tudunwada ya ce kaninsa na cikin mawuyacin hali sakamakon mummunan rauni da matar ta yi masa wanda kuma ya shafi huhunsa.
Ya zuwa yanzu dai ba a ji martanin matar da ake zargi da aikata hakan ba, wadda 'yan sanda suka ce sunanta Hauwa'u Bilyaminu. A cewarsa: "Ita matar tashi ta dauki kwalba, ta fasa masa ita ga kai. Yana dagowa haka sai ta daga masa ita ga kirji, ga gaba wadda yake cewa wurin ya samu rauni mai zurfi.
"Wanda yake cewa idan aka sa kamar dunkulen hannu yana iya shiga cikin jikin shi, har ya zamanto cewa likitoci sun ba mu dama a je a yi mishi x-ray (hoton cikin jiki).
Yusuf Abubakar ya ce an ga sashen huhunsa na gefe duk jini ya taba shi, amma dai ga shi ana fitar da jinin kuma likitoci sun ce zai rayu.
Ya ce abin da suke hasashen ya faru tsakanin mijin da matar da ake zargi, shi ne rashin ba ta izinin zuwa caji ofis don ganin halin da wani dan'uwanta yake ciki a hannun 'yan sanda.
"Akwai wani dan'uwanta da ya yi wani laifi (kuma aka tsare shi) ga ofishin 'yan sanda. Sai ya zamanto sun tafi su gane shi don su kai mishi abinci. Suka zo suka gane shi sai suka dawo.
"Wayewar yau (Laraba) da safe, sai ta ce tana so je ofishin 'yan sandan sai ya ce mata a'a. Kin ga na dawo wurin aiki, zan dan kishingida. Ki bari sai an jima," in ji Yusuf Maga-yaki.
To ga namu hasashe wannan abu shi ya sa haushi ya kama ta, sai kawai ta dauki kwalba ta daka masa, a cewar yayan mijin. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu ya ce tuni suka kama wadda ake zargin a lokaci guda kuma an kai mijin asibiti.
Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ya ba da umarni a mayar da batun hannun sashen binciken manyan laifuka don ci gaba da bincike.
"Kuma da zarar an kammala bincike ba tare da bata lokaci ba, za a kai maganar gaban kotu," in ji DSP Muhammad Shehu

No comments:

Post a Comment

Pages