Tuesday, October 10, 2017

Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale - In Ji Jaruma Rahama Sadau



Rayuwar Matan Arewa Cike Take Da Kalubale - In Ji Jaruma Rahama Sadau Daga Habu Dan Sarki Jarumar Hausa Fim Rahama Sadau ta bayyana cewar, rayuwar yar Arewa mai hankoron zama wani abu nan gaba cike take da cikas iri-iri. Sadau ta yi wannan batu ne a tattaunawa ta da jaridar Thisday. Jarumar ta ce dakatar da ita da aka yi a harkar fim din Hausa ya janyo ta sake samun wasu sabbin hanyoyi a harkar fim na cikin gida da waje. Jarumar ta ce a kullum tana kokari wajen kare mutuncinta da kuma al'adarta a lokacin da take harkar sana'ar fim na turanci wanda aka yi a kudancin Nijeriya. Sadau ta ce ko cikin kwanakin nan ta ki amincewa da yin wani fim na turanci wanda aka bukaci ta fito a matsayin 'yar madigo. ©Zuma Times Hausa

No comments:

Post a Comment

Pages