Tuesday, October 10, 2017

Mai Rahama Sadau ke shiryawa a kasar Cyprus?



Jarumar fina-finai hausa na masana'antar Kannywood ta sanya alamun tambaya ga kowa kasancewar ta a ƙasar Cyprus. A cikin hotunan da Pulse hausa ta samu zaku gan inda tauraruwar fina-finan hausa na dandalin kannywood take taya yan Nijeriya mazaunin ƙasar har da dalibai murna a bikin murnar ranar Nijeriya a ƙasar. ganin hoton muke tambaya; wata kila taje ƙasar domin shirya wani sabon fim bayan shirin RARIYA wanda ta shirya da kanta wanda yayi tasiri a kasuwa. Ko kuma ta tafi hutu ne ganin ƙasar tana da wuraren hutawa da shakatawa? Rahama wanda ta samu fitowa cikin sabbin shirin Nollywood TATU da Hakkunde kuma ta samu matsayi a shirin MTV Shuga tana morewa da nasarorin data samu sanadiyar basirar ta a harkan fim. Ku kasance tare damu domin samun asalin dalilin da ya kai ta ƙasar turai.

No comments:

Post a Comment

Pages