Monday, October 2, 2017

Kungiyar IPOB za ta maka tsohon Gwamnan Abia da Janar Buratai a Kotu


Yan Kungiyar Biyafara sun shirya da Buratai kara a Kotu - Za a hada kuma da Tsohon Gwamnan Jihar Abia Kalu - Kungiyar su na kukan bacewar Jagoran su Nnamdi Kanu Mun ji labarin cewa Kungiyar IPOB ta Biyafara za ta maka tsohon Gwamnan Jihar Abia da Janar Tukur Buratai a Kotu. Yan Biyafara su na kukan bacewar Jagoran na su Nnamdi Kanu wanda har yau ba a san inda yake ba kamar yadda Sakataren Kungiyar Emma Powerful ya bayyana. Ya kara da cewa za su shiga Kotu da Shugaban Hafsun Sojin kasar Janar Tukur Buratai domin ya fito ta Nnamdi Kanu.
Yan Kungiyar ta IPOB sun kuma soki Tsohon Gwamnan Jihar Abia Orji Uzor Kalu wanda su ke zargi da kokarin yi wa 'Yan Kungiyar su kisan gilla domin ya burge mutanen Arewa da kuma cewa ba zai rasa sanin inda aka boye Nnamdi Kanu ba. Ana dai zargin irin su Gwamna Rochas Okorocha da Ikpeazu da kokarin murkushe 'Yan Kungiyar ta ta IPOB.

naijhausa

No comments:

Post a Comment

Pages