Majiyarmu ta kawo muku jerin sunayen makarantu na alfarma kuma masu nagarta da ‘ya’yan Shugaba Buhari Suka Yi. Sai da akwai babbar ‘yar Buhari mai suna Zulaihat da ta rasu a shekarar 2012 wajen haihuwa sakamakon cutar daji ta jini da ta sha fama da ita.
1) Fatima: An haifi Fatima a ranar 7 ga watan Maris, 1975. Ta yi makarantar firamare dinta a firamarin Sojojin Sama da ke jihar Legas, ta yi karatun sakandaren ta a Kwalejin gwamnati dake Kaduna wato Government College, Kaduna; sannan ta tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin ta tafi kasar Ingila domin yin karatun babban digiri dinta a harkar kasuwanci.
2) Hadiza (Nana): An haifi Nana Hadiza a ranar 23 ga watan Yuni 1981. Ta fara karatunta ne a Makarantar Essence da ke Kaduna sannan ta tafi Kasar Ingila domin Cigaba da karatunta. Ta yi Karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Buckingham duk a kasar Ingila sannan ta dawo Kaduna domin yin babban digirinta a fannin Malanta a National Teachers Institute, da ke Kaduna. Tayi digiri dinta na biyu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic.
3) Safinatu (Lami): An haifi Safinatu ranar 13 ga watan Oktoba 1983. Ta yi karatu a makarantar Essence sannan ta wuce kasar Ingila domin yin karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Plymouth, dake kasar Birtaniya da kuma Jami’ar Arden dake kasar Ingila.
4) Halima: An haifi Halima ranar 8 ga watan Oktoba 1990. Tayi Makarantar Essence sannan ta cigaba a makarantar British School ta birnin Lome dake kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Leicester duk a kasar Ingila. Daga nan ta dawo makarantar koyan aikin lauya a Najeriya.
5) Yusuf: An haifi Yusuf a ranar 23 ga watan Afrilu. Ya yi karatunsa ne a Kaduna International School; British School ta birnin Lome a kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da Jami’ar Surrey, duk a kasar Ingila.
6) Zahra: An haifi Zara ne ranar 18 ga watan Disemba 1994. Ta yi karatunta a makarantar Kaduna International School; British School ta birnin Lome a kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Surrey duk da suke kasar Ingila.
7) A'isha (Hanan): An haifi A'isha a ranar 30 ga watan Agusta 1998. Tayi karatunta a makarantar Kaduna International School.
8) Amina (Noor): An haifi Noor ranar 14 ga watan Satumba 2004. Tayi karatu a Kaduna International School.
Binciken ya bayyana nuna cewa mafi yawancin 'ya'yan shugaban kasar sun yi karatun su ne a makarantar Kaduna International, kwalejin Bellerby's dake kasar Ingila da kuma makarantar British School ta birni Lome dake kasar Togo wato jamhuriyyar Benin.
Source :-Naijhausa
No comments:
Post a Comment