Friday, October 6, 2017

Haduwar Sanata kwankwaso da wani direban jirgin sama a Abuja


Wani direban jirgin sama da Kwankwaso ya taimaka ya tuka shi Abuja zuwa Legas - Direban na daya daga cikin matasan da Kwankwaso ya kai karatu kasar waje Alheri gadon barci, yadda ka shimfida shi, aka zaka kwanta akansa, haka zalika Hausawa na cewa abinda ka shua, shi zaka girba, in hairan hairan, in sharran sharran. Tabbas alheri gadon barci, tunda tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kwanta akan nasa yadda yayi shimfidar.
Me karatu a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba ne Sanata Rabiu Musa Kwankwaso akan hanyarsa ta zuwa jihar Legas daga babban tarayya Abuja, ya hau jirgin sama na wani kamfani mai zaman kansa, kamar yadda Umar Tanko Yakasai ma'abocin Facebook ya bayyana.

Sai dai cikin ikon Allah, ashe direban jirgin na daya daga cikin matasan da Sanata Kwankwaso ya tura su karatun koyon tukin jirgi kasar Jordan su 100, a zamanin dayake gwamnan jihar Kano karo na biyu, daga 2011-2017.

No comments:

Post a Comment

Pages