
Sanannen Furodusan nan na Fina finan Kannywood, Usman Mu’azu ya musanta zargin da yaron shahararren jarumin nan, Malam Warangis, Ibrahim Warangis yayi, na cewa wai yan Fim basu taimakesu ba. Usman yace wannan magana ba haka take ba, saboda da wasu daga cikin yan Fim suna ba Warangis tallafi iya kokarinsu, inda ya kara da cewa, wasu sun bashi taimakon a fili, wasu kuma sun boye taimakon da suka yi masa.
KARANTA:- Kannywood -Rahama Sadau Ta Turawa Mawaki classic Sako
Jaridar Rariya ta ruwaito Usmana yana kokawa kan yadda aka yi ma yan Fim kudin goro ana cewa wai duk basu taimaka ma Malam Warangis ba, wanda ke fama da cutar koda tun da dadewa.“Ni da kai na, wata jaruma data bukaci in boye sunanta ta sanya na aika masa da kudi da kuma kayan abinci, haka zalika Ali Nuhu, Sadik Sani, Zainab Ziya’u, Sa’eed Nagudu duk sun taimaka masa.” Inji Usman. Usman ya bada tabbacin akwai wasu yan Fim da suka shiga mawuyacin hali fiye da na Warangis, kuma yan Fim suna taimaka musu, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.
No comments:
Post a Comment