Sunday, October 8, 2017

El-Rufai ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben shugaban kasa a 2019


- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana wanda zai mara wa baya a zaben 2019 - El-Rufai yayi alkawarin mara wa Buahri a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2019 - Yan APC akida sun yi alkawarin hana APC jihar Kaduna tsayar da Elrufai kadai a matsayin dan takarar gwama a 2019 Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai ya bayyana cewa, shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna sun yanke shawarar mara wa shugaban kasa Muhammadu baya a zaben 2019. El-Rufai ya bayyana haka ne a wata taro da gwamnatin jihar Kaduna ta hada a ranar Asabar. Anyi taron ne saboda shiryeshiryen gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2018.
El-Rufai Ya ce: “Yan Kaduna da shugabannin jam’iyyar jihar suna bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019, da ikon Allah Buhari zai samu nasara.
“Ina rokon ku da ku cigaba da yi wa shugaban kasa adu’a, Allah ya ba shi lafiya da karfin jiki, saboda ya cigaba da shugabancin sa na adalci. Bayan haka wasu daga cikin yayan jam’iyyar APC da ke kiran kan su APC akida sun yi alkawarin hana jam’iyyar su tsayar da El-Rufai a matsayin takarar gwamna jihar shi kadai a zaben 2019.

No comments:

Post a Comment

Pages