Mun kawo jerin wasu ayyuka 25 da Gwamnatin nan za tayi - Za a gina tituna dabam-dabam a kowane bangare na fadin kasar - Yankin Kudu-maso-kudu ne su ka fi samun kaso mafi tsoka Dazu mu ke samun labari irin ayyukan titunan da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zai gina a barin kasar nan.

Za a dai yi wannan aiki ne da kudin da aka samu na hannun jarin nan na ‘Sukuk’ a kowani yanki na Kasar da kudi kusan Naira Biliyan 17. Gwamnatin Tarayya za tayi aiki na sama da Naira Biliyan 100 cur!
KARANTA:- Bayan Ali Nuhu da sadik Sani sadik ba wanda ya taimakawa mahaifina a cikin yan Fim -Yaron wargise
Yankin Arewa maso tsakiya za su samu tituna 5 daga ciki akwai titin Abuja zuwa Lokoja da kuma hanyar Suleja zuwa Minna. ,Yankin Arewa maso gabas kuma za su ga an fadada hanyar Kano zuwa Maiduguri
A Yankin Arewa maso yamma za a buda hanyar Kano zuwa Maiduguri da kuma ta Kano zuwa Kaduna da sauran su.
Yankin kudu maso gabas kuma za su ga canji a hanyar Onisha zuwa Enugu da kuma hanyar Enugu zuwa Fatakwal.
A kudu-maso-kudu za a gyara titin hanyar Garin Otuoke da kuma hanyar Lokoja zuwa Benin.
A bangaren Kudu-maso-yamma za a gyara titin Ilorin zuwa Ibadan da hanyar Garin Shagamu da sauran su.
No comments:
Post a Comment