Yanzu haka tsohon Dan wasan bayan Kungiyar Real Madrid Ricardo Carvalho ya ga ta kan sa bayan da aka yanke masa hukuncin dauri a gidan maza na watanni 7 bayan ya tabbatarwa da Kotu cewa bai da gaskiya.
Dan wasan ya furtawa Kotu da bakin sa cewa ya aikata laifin da ake zargin sa da shi na kin biyan wasa kudin haraji na sama da fam rabin Miliyan na Euro a lokacin da yake buga kwallo a Madrid daga shekarar 2011 zuwa 2013. Haka kuma an ci ‘Dan wasan da yanzu yake taka leda a Kasar Sin tara na sama da fam 140,00. Sai dai tun da wannan ne karo na farko da aka samu ‘Dan kwallon da laifi da kyar zai yi zaman kaso. Ana dai zargin wasu ‘Yan wasan na Real Madrid da kin biyan haraji.
No comments:
Post a Comment