Sunday, September 24, 2017

SUKUK: Menene SUKUK? Dalilin Bullo da shirin a Najeriya


Mutane da dama basu da masaniya game da shirin SUKUK da amfanin da zai yi wa kasa Najeriya. Shirin SUKUK shiri ne na bada takardun lamuni babu kudin ruwa a kansu. Zaka iya siyan takardan kaima domin saka jari ga wani aiki na gwamnati wanda idan kayi haka bayan duk watanni shida za a dinga biyanka da ga kudin da aka samu daidai darajar takardar da kasiya kuma babu riba a ciki. Mutanen kasa da dama suna so su saka kudin a irin wannan shiri na gwamnati sai dai kash, ganin cewa akwai riba a cikin kudaden da za a biya bayan mallakar irin wadannan takardu na saka jari ba a yi. Gwamnatin Najeriya ta kammala shirin bullo da wannan shiri na SUKUK domin ba mutane daman mallakar wannan takarda na lamuni da taimaka wa wajen gina kasa kamar hanyoyi, gidaje da sauransu. Duk da cewa kiristocin Najeriya sun fusata akan bullo da shirin cewa wai shiri ne na maida Najeriya kasar Musulunci. Abin ya tada wa majalisar koli na addinin Musulunci hankali inda ta ragargaji kungiyar CAN cewa ta maida hankalin ta wajen neman tada fitina a inda bashi. Majalisar ta ba kungiyar misalai da shirye shirye na gwamnati da dama da basu da alaka da musulunci amma kuma musulmai basu ce uffan ba sai kawai maganan SUKUK da kasashen duniya da dama da ba ma na musulmai bane suke amfani da shi zasu fito suna korafe-korafe akai. Gwamnati zata siyar da takardun lamuni na SUKUK da ya kai Naira biliyan 100 kuma koya ya siya za a biyashi duk wata shida kamar yadda Shirin yake. A Afrika da Turai da yankin Asiya duk ana ta hada-hadar SUKUK. Kenya, Tanzaniya, Afrika ta Kudu, Ingila, Luxembourg, Rasha, China, Singapore da wasu kamfanin Amurka duk sun yi nisa da zurfi a cikin tsarin SUKUK.

No comments:

Post a Comment

Pages