Atiku Abubakar ya yi kira da a kara kaimi wajen samar da dabarun ci gaban 'yan kasar masu karamin karfi: "Dole mu cigaba da aiki tukuru domin fadada hanyoyin wanzuwar tattalin arziki ga 'yan Najeriya." Ya karkare sakon nasa da cewa: "Sai lokacin da dukkan 'yan Najeriya za su iya cin abinci sau uku a rana ne za a ce koma bayan tattalin arziki ya kare. Muna da sauran aiki a gabanmu". Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin ciki da farfadowar tattalin arzikin Najeriya, bayan dawowarsa daga jinya a birnin Landan. Ya ayyana hakan ne bayan ya gana da Ministar Kudin kasar, Kemi Adeosun da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare Sanata Udoma Udo Udoma da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasar (CBN) Godwin Emefiele. Masana da yawa da suka hada da wani masanin tattalin arziki a Nijeriya, Farfesa Garba Ibrahim Sheka sun ce tattalin arzikin Nijeriya na tafiyar hawainiya bayan hukumar kididdiga ta ce kasar ta fita daga matsin tattalin arzikin da ta yi fama da shi.
Wednesday, September 6, 2017
Sai 'yan Najeriya sun koshi zan yarda tattalin arziki ya farfado — Atiku
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment