Friday, September 1, 2017

Hukumar EFCC tana binciken kadarorin ýan Najeriya su 22 a Dubai


Hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC ta samu cikakken bayanai kan wasu yan Najeriya su 22 wadanda suka mallaki manyan kadarori a kasar Dubai. EFCC na binciken mutanen ne kan zargin da suke yi musu na amfani da dukiyar gwamnati wajen azurta kawunansu, yayin da sanya idanu kan wasu gaggan yan siyasa da suka samu bayanansu daga wajen hukumomin kasashen Dubai. Wata majiya mai karfi ta shaida ma jaridar The Nation cewa “Dangane da dokokin mallaka, mun samu cikakken bayanai kan wasu yan Najeriya dake kasar Dubai, haka zalika mun samu wani jerin sunayen yan Najeriya da muke bincika a yanzu.

An samu wannan bayanai ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattafa hannu kan yarjejeniyar kwato arzikin gwamnati da aka sace,a satin data gabata..” Inji majiyar. NAIJ ta ruwaito shugaban kasa Buhari ya rattafa hannu kan yarjejeniyar ne da nufin zaburar da hukumomin yaki da rashawa na Najeriya tare da samun goyon bayan kasar Dubai wajen dawo da arzikin kasa da aka sace aka kai can.

No comments:

Post a Comment

Pages