Fitaccen jarumin nan na wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood ya koka akan yadda yan bakin ciki da mummunar adawa suka taso shi gaba da yi masa sharri da kage kala-kala duk don dai su ga sun disashe hasken tauraruwar sa. Jamrumin dai yayi wannan ikirarin ne a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu da ta tambaye shi gaskiyar labarin cewa hukumar nan ta masu shirya fina-finai ta MOPPAN za hukunta shi bisa yin kari akan abun da aka umurce shi a cikin fim watau 'over acting' a turance.
Majiyarmu dai ta samu cewa jarumin ya kada baki inda yace hakan ba gaskiya bane kwata kwata don kuwa yana daga cikin shugabannin kungiyar ma. Jarumin ya kuma ce tuni ma dai ya karyata zancen a cikin wata fira da yayi a gidan Rediyo inda yace tabbas wasu ne da ba su so suga yana ci gaba ne suke yayata wadannan labaran. Da majiyar ta mu ta tuntubi Sakataren kungiyar ta MOPPAN mai shuna Salisu Muhammad Officer, shima dai ya bayyana cewa labarin bai da tushe balle makama.
No comments:
Post a Comment