Friday, September 1, 2017

Barka da Sallah: Fasto a Kaduna ya dadada ma Musulmai da kayan Sallah


Wani Fasto a jihar Kaduna, Fasto Yohana Buru ya baiwa Musulmai gajiyayyu, musakai da marasa galihu taimakon kayan Sallah a yayin bikin Sallah babba. Fasto Buru wanda ya baiwa sama da mutane 1000 wannan tallafi yace yayi haka ne domin faranta musu rai a yayin da ake gudanar da bikin Sallah, inji rahoton Daily Trust. Cikin kayayyakin da Faston ya rabar sun hada da lemun kwalabe, sabulai da kuma abinci, inda yace yayi haka ne don cika manufarsa na taimaka Musulmai gajiyayyu don su samu walwala a yayin bukukuwan Sallah.

Daga karshe Buru ya bukaci da ya dace a inganta dangataka tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kirista, inda yace dukkanin mabiya addinan yan uwan juna ne. Majiyarmu ta ruwaito shugaban gajiyayyun, Muntari Saleh ya gode ma Faston, kuma yayi addu’ar Allah ya saka masa da alheri.

No comments:

Post a Comment

Pages