Monday, September 4, 2017

Abin Al'ajabi: Sunan Allah ya bayyana a jikin naman ragon layya


Mun kawo muku rahoton wani bawan Allah da yayi gamo da sunan Allah a jikin wasu tsokoki guda biyu na ragon su na layya, inda ya bayyanawa duniya wannan abun al'ajabi a shafin sa na dandalin sada zumunta Wani dan kasar Najeriya ya yi gamo da abin al'ajabi, yayin da sunan Allah mai girma ya bayyana a jikin wata tsokar nama ta ragon layya da suka yanka a bikin babbar sallar da ta gabata kwanaki kadan. Shi dai wannan bawan Allah, wanda yake amfani da sunan Abdullateeph Da Prince Adeyemie a shafin sa na dandalin sada zumunta, ya bayyana cewa, yayi gamo da sunan Allah ne a jikin soyayyar tsokar nama ta ragon su na layya, inda ya dauki hotuna kuma ya watsa a shafin sa na Facebook. Ya kuma rubuta a shafin na sa cewa: "Wallahi na shaida babu wani sarki sai Allah. Na saba jin zantuttukan bayyanar sunan Allah akan abubuwa da dama. Amma yau, na tabbatar da kaina." "Sunan Allah ya bayyana a jikin wata tsokar nama ta ragon mu na layya bayan an soya, kuma wannan shi yake nuna kadaitakar Allah da kuma buwayarsa. Sunan ya bayyana a jikin tsokoki biyu. #AllahuAkbar"

No comments:

Post a Comment

Pages