Tuesday, August 29, 2017

Yadda Barayi sun kai hari gidan man NNPC sun raba kyautar mai ga masu mota a Katsina


Yadda Barayi sun kai hari gidan man NNPC sun raba kyautar mai ga masu mota a Katsina Barayi sun kai hari gidan man NNPC dake jihar Katsina - Sun raba kyautar mai ga masu mota - Sannan sun kuma kwashe cinikin da akayi A daren ranar Asabar, barayi sun rarraba kyautar man fetur ga masu motoci a hanyar Katsina/Jibia bayan barayin sun kai farmaki gidan man NNPC dake a hanyar, sannan kuma suka kwashe cinikin da akayi a gidan man. Idon shaida ya bayyana cewa al’amarin ya auku ne da misalin karfe 8 na dare. Idon shaidan ya ce masu motocin sun shiga shan mai ne a lokacin da barayin suka kawo farmakin, barayin sun yi irin shigan jami’an tsaro ne. Bayan haka sun kwashe cinikin da akayi a gidan man ba tare da sunyi wa kowa rauni ba.

No comments:

Post a Comment

Pages