Wata sabuwa: Wata akida ta bayyana masu daura Qur’ani a kai suna addu’a

- Wasu kungiyar addinin musulunci sun fito a jihohin Arewa - Mutanen suna daura Qur'ani a kai suna yin addu'a Tabbas, in da ranka, ka sha kallo, an samu wata sabuwar akida a Najeriya masu karatun Qur’ani daure akansu, sa’annan su yi addu’a a haka, inji rahoton jaridar Rariya. Majiyar NAIJ.com ta ruwaito ita wannan sabuwar akidar suna taruwa ne a cikin Masallaci, inda suke zama sahu sahu, suna gabatar da addu’o’i yayin da Qur’ani ke duare akawunansu.

Sai dai wannan sabuwar akidar ya janyo cecekuce a tsakanin al’umma Muslmai, yayinda wasu ke mamakin shin wannan wani irin kungiiya ne, kuma shin ya halasta a addinin Musulunci? Kuma wanene ya kawo wannan akidar? Da wannan ake kira ga malamai dasu ilimantar da jama’a Musulmai a kan wannan akida, tare da amfaninsa ko illolin dayake tattare da su.
No comments:
Post a Comment