Wani mai shekaru 40 ya ja hankalin wata daliba da burodi,sannan yayi lalata da ita

An gurfanar da wani mutum mai shekaru 40, Kehinde Gabriel, a gaban Kotun Majistare a Jihar Lagos a Ikeja, saboda zargin lalata da wata yarinya mai shekaru uku a garin Onaosa, a yankin Ibeju-Lekki Gabriel makwabcin iyayen 'yarinyar ne dan asalin Jihar Ogun. Jaridar PUNCH ya fahimci cewa an bar yarinyar ne a baya a lokacin da take zuwa masallaci tare da 'yan uwanta a ranar 16 ga watan Agustan shekara ta 2017, shi kuma wanda ake tuhuma ya samu ya janyo hankalinta. Gabriel ya samu jan hankalinta ne bayan yayi amfani da burodi da abin sha, ya kaita dakin sa sannan yayi lalata da ita. Mahaifiyar yarinyar ta shaida wa 'yan sanda cewa yarinyar ta dawo gida tana kuka, sannan aka gano jini a gabanta. Ta ce, "Ta tafi masallaci tare da 'yan uwanta a wannan rana. Bayan 'yan mintoci kaÉ—an, ta dawo gida tare da kwalba mineras da burodi, tana kuka." Amma wanda ake tuhuma ya ki amincewa da aikata laifin, ya ce ya ba wa yarinyar abinci ne saboda tana ta kukan yunwa. Ya ce, "Na ga yarinyar tana kuka kusa da gidana kuma na tambayeta abin da ya faru da ita. Ta ce tana jin yunwa kuma na ba ta burodi da wake. Ban yi lalata da ita ba. " Wani sifeto na 'yan sanda, mai suna Saminu Imhonwa, wanda ya gabatar da wanda ake tuhuma a gaban kotun, ya ce laifin na karkashin sashe na 137 na dokar laifuka ta Jihar Legas 2011. Cajin ya karanta cewa, "Kai,Kehinde Gabriel, a ranar 16 ga watan Agusta, 2017, a layin Ogunse,Onaosa, Ibeju-Lekki, Legas, a Jihar Legas Magisterial District, kayi lalata da wata mai shekaru uku, don haka ka aikata laifin da ake zargi. A karkashin sashe na 137 na dokar laifuka ta Jihar Legas, 2011. " Babbar mai shari'a, Mrs. B.O. Osunsanmi, ta bayar da belin wanda ake tuhuma a cikin N500,000 tare da "shaidu biyu masu daraja" kowannensu da irin adadin kuÉ—in. Osunsanmi ta kara da cewa wajibi ne su bayar da shaidar biyan haraji na shekara biyu ga Gwamnatin Jihar Legas. Ta kuma dakatar da wannan karar har zuwa Oktoba 17 2017, kuma ta umurci cewa a shigar da takardun shari'ar zuwa Kotu na Shari'ar Jama'a don shawara ta doka.
No comments:
Post a Comment