Tsohon ministan kwadago ya bayyana yadda aka sace shi
Tsohon ministan kwadago da aikace aikace da ‘yan bindiga suka sace ya bayyana yadda aka sace shi - Tsohon ministan ya ce an sace shi tare da maitaimaka masa a gidansa yayin da suke cikin gonarsa kusa da Akwanga - Wata majiya ta shida cewa iyalan tsohon ministan sun biya kudin fansa kafin a sake shi. Tsohon ministan kwadago da aikace aikace, Hussaini Zanwa Akwanga, ya yi magana game da sace shi da wasu ‘yan bindiga suka yi, ko da yake har yanzu ba gano su ba. Da yake jawabi ga 'yan jarida a garinsa, tsohon ministan ya ce an sace shi tare da wani maitaimaka masa a gidansa wanda ake kira Ali yayin da suke cikin gonarsa kusa da Akwanga a hanyar Wamba da ke jihar Nassarawa.
Ya bayyana cewa"Ina godiya ga gwamnatin jihar Nasarawa, sarakunan gargajiya da sauran 'yan Najeriya don addu'o'in su da kuma gudunmawar su ganin mun dawo cikin lafiyarmu”.
No comments:
Post a Comment