Thursday, August 3, 2017

Kungiyar izalah zatayi taron bude gidan baki mallakarta a Abuja

Kungiyar Izalatil bid’a wa ikamattu sunnah na gayyatar ‘yan uwa Musulmai zuwa wajen kaddamar da sabon gidan baki da ta gina mallakarta a bababn birnin Tarayya, Abuja. Gidan ya kasance katafare mai manyan falo guda hudu da dakunan alfarma guda 20, sannan an kashe kudi kimanin N2,15,000.000.00 wajen gina shi. A cewar rahotanni an harhada kudin ne ta hanyar fatan layyana na shekara biyu da mabiya kungiyar suka harhada a fadin Najeriya da kuma tallafi daga wasu daidaikun mutane. Tuni dai aka sanya ma gidan suna wato ‘Gidan Shekh Abubakar Mahmud Gumi Jibwis Guest House’ wanda ke unguwar Life Camp birnin Abuja. Gidan na dauke ne da sassa guda hudu, inda aka sanya wa ko wani sashi suna.

Dan haka shugaban Izala Sheikh Abdullahi Bala Lau yake gayyatar ‘ya’yan kungiyar a cikin Najeriya da su halarci taron bude sabon gidan saboda su ga amfanin abubuwan da suke tarawa.

Read more: An Kaddamar da Kamfanin Sarrafa Shinkafa a Jihar Kebbi

Za’a gudanar da taron bude gidan ne a ranar 5-August-2017. Da misalin karfe 10:00 na safe. A cewar Arewablog.com shugaban na Izala ya bada sanarwar cewa, duk wanda zaizo wajen bude sabon gida to ya taho da gudunmawar Naira dubu daya.

-Naijhausa

No comments:

Post a Comment

Pages